27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tausayi ya sa an yiwa wata mata mai rainon marayu 3 kyautar gida sukutum, bayan an kore su a gidan haya

LabaraiTausayi ya sa an yiwa wata mata mai rainon marayu 3 kyautar gida sukutum, bayan an kore su a gidan haya
  • Wata mata mai ‘ya’ya uku, mai suna Ebony Johnson, wacce mai gidan hayansu ya koreta ta samu babbar kyauta a ranar Kirsimeti
  • Suzanne kawarta ita ce ta ceto ta daga halin kangin rayuwa inda tayi gaggawar nemawa kawarta taimako a wurin wasu kungiyoyi
  • Jim kadan bayan haka, ne aka mallakawa Ebony gida mai cike da kayan daki wanda ya sanya ta jin dadi

Wata mata, mai suna Suzanne Burke, ta yi wa kawarta mai suna Ebony Johnson gata, a lokacin da ta samu labarin cewa an kori kawarta daga gidan da take haya.

Suzanne ta ce ya kamata dole ta yi wani abu dan ganin ta ceto kawarta Ebony. Suzanne ta ce kawarta tana bukatar muhalli mai kyau inda zata zauna da ‘ya’yan ta.

Tana da kishin aikin ta sosai

Kawancen su ya fara ne shekara 3 da suka gabata lokacin da suka hadu a wurin aiki.

Tausayi ya sa an yiwa wata mata mai rainon marayu 3 kyautar gida sukutum, bayan an kore su a gidan haya
Tausayi ya sa an yiwa wata mata mai rainon marayu 3 kyautar gida sukutum, bayan an kore su a gidan haya

Suzanne ta ce yadda kawarta ke son aikinta abun yana burgeta kuma shine abunda ya kara karfafa zumuncin su. Lokacin da Suzanne ta lura cewa kawarta Ebony ba ta zo aiki ba kusan mako daya, sai ta yanke shawarar zuwa ta dubo ta ko lafiya, kamar yadda tashar YouTube ta 9 News ta ruwaito.

Suzanne ta dauki Mataki

Isar ta gidan ta fahimci cewa fa an kori kawar ta daga gidan da take haya, kuma ba ta da inda za ta je. Shine Suzanne ta kai korafi gun ƙungiyoyin, Allah kuma yasa korafi ya karbu aka mallakawa kawarta gida cike da kayan alatu.

A ranar da aka zo mallaka mata wannan gida ranar Juma’a 3 ga watan Disamba hawaye sun kasa tsayawa a idonta, Ebony kawai ta fashe da kuka saboda ba ta ta ba tsammanin wannan abun alkhairi ba.
Ta ce:

“Ina matukar godiya yau gamu Allah ya mallaka mana gida. Karfin addu’a ya taimakeni Allah ya dubeni da idon rahama ya mallaka min gida. ‘Zan iya komawa kafin kirsimeti?” Ebony ta ke tambaya.

Hausawa suka ce na Allah basa karewa, lallai wannan kawa ta yi bajinta sosai tare da kungiyar da suka tallafa mata, mallakar muhalli lallai abun farin ciki ne balle kuma ace kyautar sa aka maka baki daya. Wannan baiwar Allah lallai taga gata, ta kuma ga soyayya. Dama soyayya ba dole sai dan uwanka ba, akwai na Allah da yawa cike a gari.

Masu karatu wane irin fata za ku yiwa wannan kawa mai halacci, mai kokarin share hawayen duk wanda ya rabe ta?

Tausayi ya sa an budewa matar da take aikin tura ruwa a baro shagon sayar da kaya

Mutanen kasar Kenya sun nuna halin su na kulawa da taimako, bayan sun taimakawa wata mata da aka nuno tana aikin sayar da ruwa a baro a garin Dagoretti, na jihar Nairobi dake kasar ta Kenya.

Hoton matar mai suna Everlyn Ndinyuka, tana tura katuwar baro cike da jarkokin ruwa ya sanya tausayi sosai a cikin al’ummar yankin, musamman ma wata mai son taimako mai suna Wanja Mwaura wacce ta taimaka mata.

Ta cika burin ta

Ndinyuka ta bayyanawa Wanja cewa ita babban burinta shine ta bude shagon sayar da kayan abinci, ai kuwa Wanja wacce dama halayyarta ce taimakawa masu karamin karfi, ta cikawa matar nan burinta.

A ranar Alhamis 22 ga watan Yuli ne dai Wanja ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook, inda take bayyana cewa sun budewa Ndinyuka shago.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe