36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ni na dauki nauyinta har ta gama karatu – Cewar saurayin da budurwarsa ta cinyewa kudi ta je tana soyayya da wani

LabaraiNi na dauki nauyinta har ta gama karatu - Cewar saurayin da budurwarsa ta cinyewa kudi ta je tana soyayya da wani
  • Wani dan Najeriya da budurwarsa ta juya masa baya a ranan da ya bayyana mata muradin sa na son aurenta
  • Mutumin ya bayyana cewa, abin takaici ne yadda ya ga ma hidima da dawainiya da budurwar na tsawon shekara 4, kudin makarantar ta ma shi ya dauki nauyi amma ta tsefe ido ta, guje shi
  • Cikin hawaye ya bayyana dalilin da ya sa ya kunyata bayan ya kamata da wani a ranar bikin zagayowar haihuwar ta

Wani dan Najeriya da budurwar sa ta kunya ta shi a ranan da ya zo bayyana mata kudurinsa na neman aurenta hakan ya sa yaji ransa ya baci in da ya fito duniya, ya fallasa wasu sirrika da ba kowa ya sani ba. Hakan ya sa mutumin hargitsa taron murnar zagayowar haihuwarta a garin Abuja a bisa dalilin ganinta da wani da ya yi.

A wani bidiyo da ya bayyana mutumin wanda ya kasance sana’arsa gyaran waya, ya bayyana cewa shekarar su hudu suna soyayya da yarinyar.

Saurayin da budurwa ta juyawa baya
Saurayin da budurwa ta juyawa baya

A cewar mutumin da ya ke magana cikin fushi da bacin rai ya halarci wani bikin murnar zagayowar haihuwar ta ne, kawai yana shiga wurin sai ya hangeta tare da wani saurayi. Duk da wannan bakin cikin hakan bai hana shi hango, farar rigarsa sanye a jikin wannan saurayin ba tare da agogon sa. Hakan ya kara fusata shi ya tunkare su gadan-gadan don ya karbo kayansa. Ya na magana ya na kokarin mai da hawayen da ke kokarin zubo masa.

Dan kasuwar ya bayyana cewa shi ne fa ya dauki dawainiyar ta a makaranta duk wata hidimar makarantar ta shi ya ke yi mata.

Ga wasu daga cikin ra’ayoyin mutane ga me da lamarin

Wannan lamari ya jawo kace-nace matuka a shafukan sada zumunta, inda mutane suka dinga bayyana ra’ayoyin su kan halin da wannan budurwa ta jefa saurayin.

@odinny ya ce:

“Wannan mutumin gaskiya ba a kyauta masa ba Allah Ya saka masa shekarun da ya bata. Ga yana ta kashe kudinsa don ganin ya kyautata mata ashe duk a banza hankalinta yana kan wani, amma kuma bata bar kudinsa ba. Duniya mai abun mamaki. Ya gama daura burinsa a kanta, ya manta da ita kawai.”

@asiwajulerry ya ce:

“Nuna kulawa da tallafawa ga macen da ka ke so a wannan zamani, ya na nema ya zama abu mai wuya duba da irin yadda muke ganin ana yada abubuwa makamantan haka a yanar gizo.”

@ayomideadewunmi ya ce:

“Na yi matukar tausaya maka da irin wanan jarrabawa da ka shiga Allah ya baka wacce ta fita, wacce zata kula da kai fiye da tunani.”

@wallpaperplace ya rubuta cewa:

“Ka gama wahalan hidimar karatun ta… kai gaskia na tausaya maka…gaskia sun maka yankan kauna.”

Hausawa su kace in gemun dan uwanka ya kama da wuta to ka shafawa naka ruwa kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah. Tabbas irin haka na faruwa wanda har yana kai shi wanda aka yaudarar ya zama sanadiyar rashin lafiya a gareshi ko kuma wani abu marar dadi ya sameshi, cin amana duk kankantar shi babu dadi ko kadan saboda wani tabo ne da yake dadewa a zuciyar mutum bai warke ba. To masoya gareku sai ku san irin soyayyar da za ku yi.

Saurayi ya yaudari budurwarsa bayan ta bashi kodar ta guda 1 an dasa ya samu sauki

Colleen Le budurwa ‘yar shekara 30, wadda take zaune a kasar Amurka, ta bayyana cewa saurayinta a wani lokaci a baya ya bukaci ayi masa dashen koda, saboda yana fama da ciwon koda mai tsanani, wanda ya sanya ake yi masa wankin kodar yana dan shekara 17.

Ta amince ta sadaukar masa da warin kodarta bayan likitoci sun tabbatar da cewa zata yi daidai da ta shi. Bayan an gama aikin ya samu lafiya, ‘yan watanni kadan sai ya ci amanarta ya gudu ya barta.

Colleen wacce take tauraruwar tiktok, ta sami dumbin masu sharhi a kan bidiyon ta da ta wallafa, wanda ta nuna jerin abubuwan rashin kyautawa da yayi mata, inda da yawa suka dinga yaba mata saboda ceto ransa da tayi kuma suna nuna ma bata dace da shi ba.

A bidiyon ta na farko, Colleen ta bayyana cewa tsohon saurayinta ya gaya mata cewa kodarsa tana aiki ne kasa da kashi biyar cikin dari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe