27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

2023: Kungiyar mambobin jam’iyyar PDP ta yi barazanar sauya sheka idan aka bai wa dan arewa takarar shugaban kasa

Labarai2023: Kungiyar mambobin jam'iyyar PDP ta yi barazanar sauya sheka idan aka bai wa dan arewa takarar shugaban kasa

Idan har jam’iyyar PDP ta kasa tsayar da shugabancin ƙasa daga Kudu, to akwai yiwuwar mambobin jam’iyyar za su fice daga jam’iyyar, in ji wata ƙungiyar PDP, Vanguard for Justice.

A baya-bayan nan dai jam’iyyar PDP ta musanta cewa ta mayar da tikitin kujerar shugaban ƙasa zuwa Arewa sakamakon ikirarin da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya yi na cewa ta yi hakan.

Jamiyya
2023: Kungiyar mambobin jam’iyyar PDP ta yi barazanar sauya sheka idan aka bai wa dan arewa takarar shugaban kasa

Sai dai ƙungiyar a cikin wata sanarwa da shugaban ta Emmanuel Nduka ya fitar, ta gargadi jam’iyyar kan mayar da wannan matsayi zuwa yankin Arewa. Ya bayyana cewa, maida shugaban ƙasa zuwa Kudu zai samar da hadin kan ƙasa, daidaito da kuma adalci.

Bugu da kari, kungiyar ta ce yadda akasarin mutanen da ke neman mulki suka koma Kudu, ya nuna cewa abin da Najeriya ke bukata a 2023 shi ne shugaban ƙasa daga Kudu.

Musamman dattijon jiha, Alhaji Tanko Yakasai; Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, da Jonathan Asake na ƙungiyar al’ummar Kudancin Kaduna, SOKAPU, na daga cikin fitattun shugabannin Arewa, wadanda suka yi kira da a mayar da shugaban ƙasa zuwa Kudu.

A cewar sanarwar, “A ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, 2022, gwamnonin da aka zaba a ƙarƙashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun gudanar da wani taro a garin Fatakwal, babban birnin jihar Rivers. Taron daya samu baƙunci babban jigo a jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike, wanda shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya jagoranta.

“A cewar gwamnonin, sun haɗu ne domin duba halin da al’ummar ƙasar ke ciki, da kuma tsara hanyar da za a bi, musamman ganin 2023 a kusa. A ƙarshen taron, gwamnonin sun fitar da sanarwar mai ɗauke da abubuwa tara, wadanda suka cimma matsaya

“Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari (dan Arewa) ta shafe shekaru takwas ta na mulki. Jam’iyyar PDP a matsayin ta na jam’iyya na shirin sake kwace mulki a Arewa. Hakan dai na iya janyo kwararowar ‘ya’yan jam’iyyar PDP da dama zuwa jam’iyyar APC, kasancewar suna ganin jam’iyyar APC ce za ta sanya shugaban ƙasa zuwa Kudu” a cewar su.

Ana gudanar da taruka na sirri da tuntubar juna a lokaci guda a jihohin Legas da Kano. Amma a lokacin da aka tuntubi masu ruwa da tsaki sun ki yin magana a kan lamarin. A yanzu dai sun ja da baya, suna cewa idan lokaci ya yi za su yi magana, kuma jam’iyya da ‘yan Nijeriya za su ga fuskokin su. Wannan na iya zama ibtila’in da za ta kawar da PDP gaba daya.

Kwanan nan tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya shaida wa ‘yan siyasa, wadanda akasarin su suna sa ran albarka da amincewar sa, cewa ya daina yin siyasar bangaranci.

Allah ba zai taba yafewa jam’iyyar PDP ba, gwamnan PDP ya fasa kwai

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya bayyanaa cewa Allah ba zai taba yafewa jam’iyyar PDP ba matukar ta kasa jin kukan da ‘yan Najeriya suke yi na bukatar ceto su daga bala’in da suke ciki.

Wike ya bayyana hakane a lokacin da ya kai ziyara ga takwaransa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ranar Asabar 1 ga wataan Janairu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe