34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Dangote ya shafe shekaru 11 a jere yana zama bakar fata na 1 da yafi kowa arziki a nahiyar Afirka da kuma duniya baki daya

LabaraiDangote ya shafe shekaru 11 a jere yana zama bakar fata na 1 da yafi kowa arziki a nahiyar Afirka da kuma duniya baki daya
  • Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, ya shafe shekara 11 kenan yana rike da wannan kambun
  • Mike Adenuga, Rabiu Abdulsamad su na cikin mutum uku da mujallar Forbes ta ambata a matsayin masu kudin nahiyar Afrika
  • ‘Yar kasuwa Folorunsho Alakija ita da yace bata samu wannan nasarar ba, bayan hauhawar arzikin ta ya ragu

Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen hamshakan attajirai wanda ta ke yi kowacce shekara a inda ‘yan Najeriya uku kacal ne kacal suka samu wannan nasarar, Aliko Dangote, Mike Adenuga da kuma Abdul Samad Rabiu.

Ta bayyana hakan ne a cikin wani sako da ta fitar a yanar gizo a ranar Litinin, inda ta bayyana jerin sunayen attajiran da suka fi kowa kudi a nahiyar Afirka a shekarar 2022, sunan mutum daya ne kawai ba tayi nasarar samun wannan kambu ba a wannan shekarar, ita ce Folorunsho Alakija.

Rahoton ya nuna cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote ya cigaba da rike kambun a matsayinsa na bakar fatar da yafi kowa arziki a duniya, inda ya ke da kudi kimanin dala biliyan 13.9. Yayin da Folorunsho Alakija arzikinta be kai ta shiga wannan sahun ba a wannan karon.

Dangote
Aliko Dangote

Ga kadan daga cikin abunda rahoton ke cewa :

“Shekaru 11 kenan a jere, Alike Dangote yana lashe kambun attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka, wanda kudin sa ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 13.9, wanda ya ninku sama da na bara inda yake da dala biliyan 12.1 a bara, biyo bayan karin hannayen jari da ya samu a bangaren siminti inda ya samu kaso 30 cikin 100. “musamman da aka samu karin yawan gine ginen gidaje a Najeriya da kuma ayyukan gine gine da gwamnati ke yi inda aka samu karuwar siyayya musamman a cikin watanni tara na farkon shekarar 2021, kamar yadda manazarta suka gano.”

Sauran sunayen da ke cikin jadawalin

Sunan da ke biyo bayan na Dangote shine hamshakin attajirin nan na Afirka ta Kudu, Johann Rupert. Sai ‘yan Najeriya biyu da ke cikin jerin wanda suka hada da Abdulsamad Rabiu wanda yazo na biyar sai Mike Adenuga shi kuma yazo na shida. Mujallar Forbes ta bayyana cewa Rabiu ya sami karuwar arziki sosai daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu.

Forbes ta ci gaba da cewa:

“Dan Najeriya nan da ya gawurta a harkar siminti Abdulsamad Rabiu, wanda ya samu karuwar arzikin na kimanin dala biliyan 1.5 bayan ya habbako da wasu kamfanonin sa.”

“A farkon watan Janairun Shekarar 2022, Rabiu ya bayyana sunan kamfanin sa na sugar da abinci BUA Foods a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya. Shi da dansa ne suke rike da hannun jarin mafi tsoka wanda ya kai kashi 96% a kamfanin, wanda a kwanan nan ne yake da jarin kusan dala biliyan 2.8.”

“(Forbes tana rage kimar hannun jari idan ribar ‘yan kasuwa bai kai kashi 5%) ba, amma Abdulsamad da dansa su ke da hannun jarin kashi 96% a kamfanin, wanda aka bayyana hakan a watan Janairun 2020.

Matatar mai ta Dangote zata fara aiki a cikin wannan shekara ta 2022

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, yace, aikin matatar man fetur ta Dangote da takin zamani, zasu kammala kafin karshen shekarar nan da muke ciki.

Ya bayyana hakan ne yayin da shugaban bankin cigaban Africa, Dr. Akinwumi Adesina, ya jagoranci ayarin wakilcin bankin, zuwa wurin matatar a garin Legas.

Matatar zata fara aikine a karshen zangon karshe na wannan sabuwar shekarar ta 2022.

“Kusan mun kammala duk wani aikin sanya injina, amma yanzu mun fara gwajin duk wani abun daya shafi bangaren ruwane inda shima Kusan Kashi saba’in 70% ya kammala. Abin da muke fata shine, wajen zangon karshe na wannan sabuwar shekarar, zata fara aiki” Inji Dangote.

Babban daraktan zartarwa a bangaren tsare-tsare, bunkasa jari, da kuma manyan ayyuka, na rukunin masana’antun Dangote, Devakumar Edwin, yace, matatar mai hadakar bangarori da suka hada da: masarrafar man fetur, masarrafar takin zamani, da kuma aikin dashen bututun karkashin kasa ; wani gagarumin aikin ginin matatar mai ne a duniya baki daya.

Edwin ya bayyana cewa, tace man fetur mai yawan kimanin ganga 650,000 ba karamin canji zai kawo ga tattalin arzikin Nageriya ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe