34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wani mutumi ya fara tattaki daga birnin London zuwa birnin Makkah inda zai shafe shekara 1 cur yana tafiya

LabaraiWani mutumi ya fara tattaki daga birnin London zuwa birnin Makkah inda zai shafe shekara 1 cur yana tafiya
  • Wani mutum mai suna Adam Muhammed, ya fara tattaki tun daga birnin London a shekarar 2021 yana fatan danganawa da birnin Makka a kafa
  • Mutanen da suka yaba da kokarin sa sun fito suna taimaka masa a kan hanyar sa da abinci da kuma wurin kwanciya
  • A cewar mai tattakin, yace zai ratsa ta kasar Syria da Jordan kuma yana fatan kammala tafiyar a watan Julin shekarar 2022

Wani mutumi dan shekara 52, mai suna Adam Muhammed ya fara tattaki tun daga birnin London dake kasar Birtaniya, yana fatan danganawa da birnin Makka a kafa. Ya fara wannan tafiyar a watan Agustan shekarar 2021.

Tun daga lokacin da ya fara tafiyar, ya dinga dora hotunan shi a yanar gizo, inda mabiyansa suka dinga yaba masa. Mutanen da suka san shi a inda yaje, sukan bashi makwanci, abinci kuma su taimakeshi wajen tura jakarsa ta hannu, kamar yadda jaridar TRT World suka wallafa.

Adam ya kara himma wajen tattaki

Ya sami damar ratsa kasashen Netherlands, Jamus, da kuma Czech Republic. Yanzu haka, yana birnin Istanbul dake kasar Turkiyya.

Adam Muhammed mai tattaki daga London zuwa Makkah
Adam Muhammed mai tattaki daga London zuwa Makkah

Adam ya kudurci aniyar sai yaje birnin Makka a kafa, tun a watan Yuli, inda ya shirya ratsawa ta kasashen Syria da Jordan.

A hotunansa da aka yada a Instagram, an nunoshi a gaban kyanmara yanata murmushi, inda mutane da dama suka dinga yin sharhi.

Jaridar Labarun Hausa sun tattaro muku wasu daga cikin sharhin kamar haka:
noenam yace,

“Ta yaya ya ratsa duka wadancan kasashe a hanyar sa ta zuwa Makka ” ko wacce kasa yaje sai yayi biza? Kawai tsegumi nakeyi.

othmanyahyadmg yace:

“Ina son irin wannan tafiya ta kasada”.

kutupyildiziiiiiii yace:

“Mashaallah danuwana Allah yai maka albarka”.

iamfarah9 tace:

“Karin nagarta gareka”.

france.mosques yace :

“Mashaallah, Allah ya saukaka maka tafiyar”.

deyn_shawket_aqcora_official yace:

“Fatan nasara dan uwana Allah ya kare ka”.

Mutumin da yake tattaki kullum zuwa wurin aiki ya sami babban tallafi

A lokaci guda har’ila yau, jaridar Labarun Hausa sun gano wani labari na wani mutum mai suna Donte Franklin, wanda yake shafe awanni kullum domin tafiya wurin aiki a kafa, ya sami tallafin da bai taba tsammani ba; ‘yan watanni da suka wuce.

Abin ya fara ne, lokacin da wani mai aikin taimakon al’umma mai suna Michael Lynn, yaga Donte din wata rana yana tafiya wurin aikin a kafa. Daya tambayeshi, me yasa yake yin hakan. Ya shaida masa cewa, yana shafe fiye da mil 8 daga gidansa zuwa wajen aikin sa, domin ciyar da iyalinsa.

Tafiyar da yake yi mai nisa daga gidan sa zuwa ‘Buffalo Wild Wings’ inda yake aiki, tana daukansa tsawon awa biyu da rabi. Amma duk da gajiyar da yayi haka zai kara nausawa ya koma gida.

Gimbiya Diana ta yi niyyar shiga addinin Musulunci Allah bai yi ba har ta koma ga Allah – Dan jaridar masarautar Ingila

Wani mai daukar hoton cikin Masarautar kasar Birtaniya ya bayyana cewa Marigayiya Gimbiya Diana ta yi kwadayin shiga addinin musulunci a inda ta dinga bi tana neman sani game da addinin Musulnci da kuma neman sani game da mai addinin ya ce akan auren wani mabiyin addini da ban.

Ta nemi wannan sani ne a lokacin da suke tafiya cikin jirgi yayin wani rangadi da za suka je, kimanin shekaru casa’in da suka gabata.

Anwar Hussein shine dan jarida mafi dadewa a gidan Sarautar Ingila

A lokacin, an ba da rahoton cewa gimbiya ta yi ta tambayar Anwar Hussein, mai kimanin shekaru 83, wanda ya kasance ɗan jarida mafi dadewa a kan harkar daukar hoto na gidan sarauta, wanda ya hada tarihin rubutun tafiyar Gimbiya Diana daga shekarar 1980 har zuwa lokacin rasuwarta a shekarar 1997.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe