34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Tsoro ya sa iyayen wanda ya halaka Hanifa tserewa daga matsugunin su

LabaraiTsoro ya sa iyayen wanda ya halaka Hanifa tserewa daga matsugunin su

Tsoro ya sanya iyayen Abdulmalik Tanko wanda ya halaka Hanifa Abubakar, tserewa daga matsugunin su.

A wata ziyara da jaridar Daily Trust ta kai unguwannin Tudunwada da Tudun Murtala inda Abdulmalik ya taso da kuma gidan mahaifan sa, maƙwabta sun bayyana cewa ba san inda iyayen na sa su ka tafi ba.

Tsoro ya sa iyayen wanda ya halaka Hanifa tserewa daga matsugunin su
Tsoro ya sa iyayen wanda ya halaka Hanifa tserewa daga matsugunin su

Wata majiya ta kusa da iyayen na sa ta bayyana cewa a dalilin ta’asar da ɗan su ya tafka ta sace Hanifa da kuma halaka ta, akwai yunƙurin kai musu hari. Wannan ya sanya dole iyayen na sa su ka tsere daga matsugunin su.

Musa Shehu (ba ainihin sunan sa na gaskiya ba) ya ce:

“Ba wanda zai iya faɗin inda suke. Sun koma wani boyayyen waje da zama. Mahaifiyar sa ta ƙi amsar ‘ya’yan sa sannan ta raba gari tsakanin ta da shi.”

Daily Trust ta ruwaito cewa Abdulmalik Tanko, mai makarantar su Hanifa, ya tabbatar da halaka ta, ta hanyar ba ta maganin ɓera.

Sannan kuma yayi mata gunduwa-gunduwa kafin ya birne ta a ɗaya daga cikin rassan makarantun sa. Yarinyar dai an sace ta ne a watan Disamba, sannan aka halaka ta kwanaki ƙadan bayan nan, duk da waɗanda suka ɗauke ta sun buƙaci a biya su miliyan 6 a matsayin kuɗin fansa.

Jami’ai sun cafke Abdulmalik a lokacin da ya ke ƙokarin ɗaukar wani kaso daga cikin kudin fansar.

Kisan na Hanifa ya fusata mutane da dama, wanda akai ta magana akan sa a kafafen sada zumunta.

Da nasan haka zai kasance da ko auren shi ban yi ba, Matar wanda ya yi garkuwa da Hanifa

Matar mutumin da aka ɗamke da laifin yin garkuwa da kuma kisan wata ƙaramar yarinya a Kano, Hanifa Abubakar ta bayyana yadda maigidan na ta ya yaudare ta ya kawo yarinyar gida kafin daga bisani ya halaka ta.

Matar ta bayyana cewa ƙarya mijin na ta ya sharara mata cewa iyayen yarinyar sun yi tafiya, shiyasa su ka damƙa masa amanarta kafin su dawo daga tafiyar da su kayi.

Ta dai bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Dala FM ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe