27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da malami da wasu mutum hudu – ‘Yan sanda

Labarai'Yan bindiga sun yi garkuwa da malami da wasu mutum hudu – ‘Yan sanda

‘Yan sandan sun bayyana sunayen mutane biyar da aka yi garkuwa da su a jihar Yobe da ke arewa maso gabas a kasar Najeriya

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a ranar Larabar da ta gabata ta tabbatar da sace Babagana Kachalla, mataimakin shugaban makarantar Central Primary Buni Yadi da wasu mutane hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Madiya da ke karamar hukumar Gujba a jihar.

Kwalawa
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da malami da wasu mutum hudu – ‘Yan sanda


Kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.

Mista Abdulkarim, mataimakin sifetan ‘yan sanda ya bayyana sunayen sauran wadanda aka sacen da suka hada da Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da kuma Hajiya Gana.

Ya ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe 8:20 na safiyar ranar Talata, Mala Boyema ne ya kai rahoton sa ofishin ‘yan sanda na yankin da misalin karfe 10:37 na safe.
Kakakin ya ce, Mista Boyema ya yi sa’a ya tsallake rijiya da baya daga garkuwar da wasu mahara dauke da muggan makamai suka yi a lokacin da ya arce da shingayen da suka yi a Madiya.

Sai dai ya ce daga bisani maharan sun sako Mista Gana.

‘Yan sanda sun kama wani matashi yana lalata da akuya a jihar Jigawa

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Shisu ya sanarwa da manema labarai cewa rundunar su ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 25 a unguwar Kunnadi dake cikin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, yana lalata da akuya.

Jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar cafke matashin ne a daidai lokacin da yake aikata masha’a da akuyar.

An ruwaito cewa saurayin ya kama akuyar da karfin tsiya ne ya fara lalata da ita har zuwa lokacin da jami’an tsaron suka iske shi turmi da tabarya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa tuni sun fara gudanar da bincike kan wannan lamari, kuma da zarar sun kammala hada bayanai akan binciken za su tisa keyarsa zuwa gaban kotu don ya girbi abinda ya shuka.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe