36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Da duminsa: ‘Yan bindiga sun sace dan uwan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

LabaraiDa duminsa: 'Yan bindiga sun sace dan uwan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Wasu mutane ɗauke da bindigu sun sace ɗan’uwan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.

Rahotanni sun nuna cewa an ɗauke Mr Robert Jepthan a daren ranar Talata a gidan sa da ke kan hanyar Dimrose, a yankin Biogbolo a birnin Yenagoa.

Yana tsaye a kofar gidan sa misalin ƙarfe 9:30 na dare, kwatsam wata mota ta tsaya kusa da shi sannan wasu mutane da su ka ɓoye fuskokin su, su ka ƙwamushe shi zuwa cikinta da ƙarfin tsiya.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni ‘yan sanda su ka fara gudanar da bincike.

“An ɗauke shi ne a hanyar Dimrose cikin birnin Yenagoa. Muna ƙara ƙoƙari wajen ganin mun ƙwato shi sannan mun cafke waɗanda su ka yi garkuwa da shi. Muna aiki kan wani abu mai ƙwari”.

Bincike ya nuna cewa satar Mr Robert ita ce satar manyan mutane na shida da ta auku a cikin watanni biyar ɗin da su ka gabata a jihar Bayelsa, duk kuwa da ƙoƙarin da hukumar ‘yan sandan jihar ke yi.

Wasu da aka sace ɗin sun haɗa da mahaifiyar magatakardan gwamnatin jihar Bayelsa, Mrs Betinah Benson, babban ma’aikacin banki Mr Tari Ajanami, mahaifin shugaban ƙaramar hukumar Ogbia, Chief Marvin Turner, shahararren ɗan kasuwa Mr Lotana Okoye da kuma sanannen ɗan kasuwa kuma kwamishinan cinikayya da zuba jari Mr Federal Otokito.

An ceto mutum 2,155 da masu garkuwa suka sace a Zamfara a cikin wata hudu

Gwamnatin jihar Zamfara tace ta tseratar da mutane 2,155 wadanda yan garkuwa da mutane suka sace a jihar, daga watan Satumba na shekarar 2021 zuwa watan Janairun wannan shekara ta 2022.

Kwamashinan yada Labarun jihar Ibrahim Dosara, shine ya bayyana hakan a garin Gusau a ranar Lahadi 23 ga watan Janairu, inda yace, an samu nasarar ne sakamakon hadin kai tsakanin jami’an tsaron da aka girke a fadin jihar.

Wadanda aka tseratar da suka hada da ‘yan makaranta, daliban firamare, mata da kuma kananan yara, tuni an sada su da ‘yan’uwan su.

“Muna nuna godiyar mu ga jami’an tsaro, saboda rubanya kokarin su a ‘yan kwanakin nan “

“Ayyukan jami’an tsaro daban-daban, na bayannan wanda sukayi a dajin Gando, ya tarwatsa yan ta’addan da suke a wurare daban-daban, kuma ya kassara karfin da suke dashi.

“Kawo karshen wannan mummunan ta’addanci, za’a iya cewa yazo kusa a irin wannan lokacin, da kuma kyakkyawan fatan da ya dara na kowanne lokaci ” Kwamashinan ya fada.

Ya kara da cewa, Gwamna Bello Matawalle yana aiki tukuru wajen ganin dawowar doka da oda a jihar, duk da kalubalen tsaro da take fuskanta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe