24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An sauke ni daga mukamin Ministar Ingila saboda kasancewa ta Musulma, kuma nace Allah daya ne – Nusrat Ghani

LabaraiAn sauke ni daga mukamin Ministar Ingila saboda kasancewa ta Musulma, kuma nace Allah daya ne - Nusrat Ghani

Tsohuwar ministar sufuri ta Birtaniya, Nusrat Ghani, tace, takura mata akayi tilas ta sauka daga mukaminta, lokacin da akayi garan bawul a gwamnatin Birtaniya, a shekarar 2020, kawai dan ita Musulma ce.

A cewar yar jamiyyar ra’ayin rikau din (conservative ), kuma yar zauren majalisa; lokacin da tana hira da jaridar Sunday Times, a ranar Litinin.

Nusrat Ghani ta zama mace ta farko a cikin jami’an gwamnatin Birtaniya a shekarar 2018

A shekarar 2018 Nusrat Ghani ta zama mace ta farko a cikin kunshin jami’an gwamnatin Birtaniya. Ta zama ministar sufuri a gwamnatin, a karkashin babban minista, Theresa May.

Amma a watan Fabrairun shekarar 2020, sai aka fitar da Nusrat Ghani din daga jerin kunshin gwamnatin, yayin da sabon babban minista Boris Johnson ya kafa sabuwar gwamnati.

Nusrat Ghani ta shaidawa Sunday Times cewa, da ta tambayi bulaliyar majalisar dalilin da yasa aka cireta daga cikin jami’an gwamnatin, sai yace; “an bijirar da maganar musulunci a matsayin matsala, yayin da ake tattaunawa akan garan bawul din gwamnatin. Saboda haka kasantuwarta musulma, hakan ya sa da yawa basuji dadi ba”.

Nusrat Ghani, tsohuwar ministar sufuri ta kasar Birtaniya
Nusrat Ghani, tsohuwar ministar sufuri ta kasar Birtaniya

“Kasantuwarki Musulma yana da mummunan tasiri a garan bawul din. Wasu mambobin ma an wulakantasu domin sun Musulunta.”

Tace:
“Wannan kamar naushi ne a ciki. Naji haushi kuma naji kamar an zare min laka.

Dan majalisar da aka zaba daga yankin Wilden na Birtaniya , yace “za’a koreshi daga jamiyya, kuma mutuncinsa zai zabe ” Idan ya kambama maganar.

Mark Spencer ya musanta wannan magana

Bulaliyar majalisar, kuma dan jamiyyar ra’ayin rikau din, Mark Spencer, ya musanta zargin da aka fitar a ranar Juma’a, wanda yake zayyano kagen da bashi da tushe balle makama, akan Nusrat Ghani din, wanda ba tun yanzu ake fadar su ba.

“Wannan kagen gaba daya karyane, kuma ni ina ma kallonshi a matsayin bata suna” ya fada a twitter.

Spencer yace, shi bai taba gayawa Nusrat cewa an cireshi daga ma’aikata, saboda shi Musulmi bane.

A wani bangaren, ministan ilimi na Burtaniya, Nadeem Jahai, yace wannan zargin ya kamata ayi bincike akai.

A shafinsa na twitter yace, babu wani gurbi daya bada dama a jamiyyar su ta (conservative) mai ra’ayin rikau, da a nuna kiyayyar Musulunci ko wata kabila. Wannan zargi dole ne ayi bincike.

Shugaban jamiyyar adawa ta Labour party, Carestarmer yace, dole ne a bincika wannan zargi na Nusrat Ghani.

“Abin kaduwa ne a karanta irin wannan abu” data rubuta a twitter.

Tun farko a ranar, mai gabatawa na jamiyyar ra’ayin rikau, William Rudd, ya zargi babban minista da “daura masa jakar tsaba” inda yan majalisar ke san cire shi.

Gimbiya Diana ta yi niyyar shiga addinin Musulunci Allah bai yi ba har ta koma ga Allah – Dan jaridar masarautar Ingila

Wani mai daukar hoton cikin Masarautar kasar Birtaniya ya bayyana cewa Marigayiya Gimbiya Diana ta yi kwadayin shiga addinin musulunci a inda ta dinga bi tana neman sani game da addinin Musulnci da kuma neman sani game da mai addinin ya ce akan auren wani mabiyin addini da ban.

Ta nemi wannan sani ne a lokacin da suke tafiya cikin jirgi yayin wani rangadi da za suka je, kimanin shekaru casa’in da suka gabata.

Anwar Hussein shine dan jarida mafi dadewa a gidan Sarautar Ingila

A lokacin, an ba da rahoton cewa gimbiya ta yi ta tambayar Anwar Hussein, mai kimanin shekaru 83, wanda ya kasance ɗan jarida mafi dadewa a kan harkar daukar hoto na gidan sarauta, wanda ya hada tarihin rubutun tafiyar Gimbiya Diana daga shekarar 1980 har zuwa lokacin rasuwarta a shekarar 1997.

A wannan lokacin, Gimbiya Diana, wacce ta kasance tana bin addinin Kiristanci, ta fara soyayya da wani likitan zuciya Musulmi mai suna Dr Hasnat Khan. Kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito, cewa Gimbiyar ta fara tunanin shiga addinin Musulunci domin ganin ta mallaki masoyinta sunyi aure.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe