34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Matashi dan shekara 16 ya canjawa kekensa fasali zuwa babur ta hanyar amfani da injin janareto

LabaraiMatashi dan shekara 16 ya canjawa kekensa fasali zuwa babur ta hanyar amfani da injin janareto

Adewale matashin yaro ne dan shekara 16 mai matukar fasaha ta kere-kere, inda ya canjawa kekensa fasali daga keke ya mayar da shi babur ta hanyar amfani da injin janareto na wuta. Ya ce ya kashe naira dubu talatin (30000) da kuma goyon baya da ya samu daga wajen mahaifin shi yayin da mutane ke yi masa dariya…

Yaro dan shekara 16, Adewale Quoyim, shaida ne akan yadda wani tunanin fikirar kirkira na mutum zai iya bada bankaye. Ya canja kekensa zuwa babur, da tunanin sa shi kadai.

Da yake magana da BBC bangaren turancin pidgin, a wata tattaunawa, yace, mutane sunyi ta gaya masa cewa ba zai iya canja injin janareto ya koma aiki kamar babur ba.

Mahaifinsa ya karfafa masa gwiwa

Yayin da abinda mutane ke fada ke neman rage masa kwarin gwiwa, sai mahaifinsa ya kara zaburar dashi. Bayan ya kammala aikin har yana hawan kayansa sai kuma mutanen da suke ganin ba zai iya ba, suka koma suna mamaki gami da murna.

Yara masu fasaha, ciki hadda matashin da ya canjawa Keke fasali
Yara masu fasaha, ciki hadda matashin da ya canjawa Keke fasali

Dan aji uku na makarantar sakandaren, yace ya fara koyon aikin gyaran kanikanci tun yana dan shekara goma 10.

Adewale yace, ai dole ne ma ya kirkiro wannan fasahar. Saboda, yayi ta burin siyan babur, amma bashi da halin saye.

Yadda fasahar ke aiki

Yayi filla-filla da wani injin janareto, inda ya sanya wani bangare na injin a gurin feda, tankin mai yana jikin singalalin keken.

Adewalen yace ya kashe kimanin Naira dubu talatin N30,000 akan aikin. Matashin ya siyo tsohon inji ne, inda ya mai dashi yadda zai iya sarrafuwa da kuloti.

Haka kuma, ya bayyana cewa ya sha wahalar aikin, saboda babu wanda zai ce masa yi kaza ko gyara kaza.

Wasu daga cikin sharhi ga matashin

Saikou Fofana yace:

“Abun al’ajabi, Allah yai maka albarka, ka zama babban injiniya a nan gaba”

Adewale Oyebade yace :

“Babban kai.. Amma nan gaba kayi amfani da babban batiri mai karfin doki 12. wannan zaifi saukin kashe kudi. Ba sai kana zuba mai ba, ga kuma karancin gurbata muhalli .”

Tonye Pepple tace :

“Abin mamaki, basira a Afrika, yayi kyau dan uwa, fatan nasara.”

C Man Emmi yace:

“Komai mai yiwuwa ne idan ka yarda da kanka. BBC da Allah ina neman lambar wayar wannan bawan Allah daga mutanen ku. Domin in tura masa kudi. Ni daga Jamus nake.

Mutane sun dauka cewa na haukace ne – Cewar hazikin matashi da ya kera mota da kayan da yake tsintowa a bola

Wani matashi da akai ta yadawa a yanar gizo bayan ya kera mota ya ce mutane da yawa sun dauka na haukace ne. A wata hira da BBC Pidgin ta yi da shi, Amalu Chikamso ya ce a lokacin da ya fara kokarin kera wannan mota, ya kan yi yawo da ga wannan bola zuwa waccan domin neman kayan aiki. Hakan ya sa mutane su ke ganin kamar baya cikin hayyacin sa.

Ina bin bola don neman kayan aiki

Ya kara da cewa tsabar bin bola, babu bolar da ban sani ba a garin Enugu yawo na ke yi tun safe har dare.

Matashin ya kara da cewa tun yana yaro ya ke mafarkin kera motarsa har yakan hada motar wasan yara da robobi.

Chikamso ya kara da cewa, a duk lokacin da zai je makaranta, ya kan dan tsaya a wata bola ya tsinci kayan aiki saboda babu wanda ya taba tallafa masa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe