29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

A karon farko Ahmed Musa yayi magana bayan an kori Super Eagles daga AFCON

LabaraiA karon farko Ahmed Musa yayi magana bayan an kori Super Eagles daga AFCON

Ahmed Musa ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa ƙungiyar Super Eagles za ta farfaɗo daga ci bayan da ta samu a gasar AFCON ta 2021

Ƙasar Tunisiya ce ta koro Super Eagles a mintuna 16 na ƙarshe

Ahmed Musa ya yi martani yayin ga makasan Hanifa, yarinyar Kan mai shekaru 5
A karon farko Ahmed Musa yayi magana bayan an kori Super Eagles daga AFCON

Musa ya bayyana cewa kungiyar ta yi iyakar ƙoƙarin ta, sai dai hakan bai wadatar ba, inda ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za su taɓuka abin kirki a wasanni masu zuwa

Kyaftin ɗin Super Eagles Ahmed Musa, ya gode wa ‘yan Najeriya bisa ƙaunar da suka nuna wa kungiyar su duk da sun gaza wucewa zagaye na gaba a gasar cin kofin Nahiyar Afrika da ta gudana a ƙasar Kamaru.

Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan sun yi iyakar ƙoƙarin su, sai dai daga ƙarshe basu samu nasara ba.

Kungiyar wacce Augustine Eguavoen ya ke jagoranta, ta lashe dukkan wasanni ukun farko, kafin ta sha kaye a hannun Tunusiya.

An dai samu ra’ayoyi mabambanta a nan gida Najeriya bayan shan kashin, inda wasu ‘yan Najeriya suka soki kungiyar, yayin da m wasu kuma suka ƙarfafa wa ‘yan wasan guiwoyin su.

Musa ya magantu

Musa ya tabbatar da cewa kungiyar ‘yan wasan za ta yi ƙoƙari sosai a wasanni masu zuwa. Yanzu dai tawagar ta Super Eagles za ta mayar da hankali wajen cin wasan da za ta yi da ƙasar Ghana a ƙoƙarin ta na zuwa gasar cin kofin duniya ta 2022.

Musa ya yi wallafar a Facebook inda yace:

“A rayuwa, ba koda yaushe ba ne abubuwa suke zuwa mana yadda mu ke so ba, wannan wani abu ne da dole muyi haƙuri da shi komai tsaurin sa. Mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu, sai dai hakan bai ba mu damar zuwa zagayen gaba ba. Ba zamu sare ba, zamu yi abinda yafi haka a nan gaba. Mun gode da kulawar ku da kuma addu’oin ku. Mun gode matuƙa.”

Ahmed Musa ya nuna takaicinsa kan kisan yarinya ‘yar shekara 5 Hanifa Abubakar a Kano

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, yayi bakin ciki, bayan da ya samu labarin abinda ya faru da Hanifa Abubakar daga kasar Kamaru inda yake wakiltar Najeriya a gasar AFCON ta 2021.

An rawaito cewa kawun mamaciyar, Suraj Suleiman, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ya sace yarinyar ya kai yarinyar ga matarsa ​​wadda ta ki ci gaba da rike ta.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe