34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wata mata ta dambara wa mijin ta dutsen guga mai zafi wanda yayi ajalin sa a Legas

LabaraiWata mata ta dambara wa mijin ta dutsen guga mai zafi wanda yayi ajalin sa a Legas

Wata mata ta dambara wa mijin ta dutsen guga mai zafi wanda yayi ajalin sa a Jihar Legas.
Matar aure mai suna Motunrayo, ta halaka mijinta mai suna Alaba wanda aka fi sani da Bama, a yankin Abule-Egba a jihar Lagos.

Jaridar PUNCH ta samo bayanai akan cewa ma’auratan sun samu sa’insa ne a tsakanin su wanda daga baya abin ya koma faɗa kaca-kaca.

Miji da mata
Wata mata ta dambara wa mijin ta dutsen guga mai zafi wanda yayi ajalin sa a Legas

Ana zargin Motunrayo ta sanya dutsen guga a wuta inda daga bisani tayi amfani dashi wajen ƙona mijinta a ƙirjin sa bayan ya dauki zafi.

Mutumin ya mutu sakamakon raunukan da ya samu daga kunar.

Majiyar ta bayyana cewa mutumin da matar sa, tare da yaran su uku, ba su daɗe da dawowa daga hutu ba daga ƙasar Dubai.

Kafin mutuwar Alaba a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2022, shi ne mai masaukin bakin Bama da ke yankin Abule Egba.

Sai dai akwai labarai guda biyu mabambanta akan abinda ya haddasa rikici a tsakanin ma’auratan.

Wani mutum mai suna Kelly Hassino, ya shaida cewa Motunrayo ta gano cewa mijin ta ya ɗirka wa wata mata ciki ne.

A wata wallafa da yayi a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewa:

“Matar sanannen mutumin nan mai Bama hotel and suites da ke yankin Agbule Egba na jihar Legas, ta halaka shi a daren jiya yayin da yake barci bayan ta gano cewa ya ɗirkawa wata budurwa ciki!

“Bama kamar yadda akafi sanin sa da shi, ya dawo daga hutu a ƙasar Dubai tare da matar da ‘ya’yan su uku babu dadewa. Shekarun su 8 da aure kenan.

“Abin da yafi muni shi ne hanyar da ta bi wajen halaka shi. Da farko ta sanya masa kayan maye, bayan ta tabbatar da ya yi barci, sai ta sanya dutsen guga a wuta inda ta tabbatar ya dauki zafi sosai sannan ta ƙona shi a sassa daban-daban na jikin sa har saida ta tabbatar ya mutu.

“Wannan kisa ne mai raɗaɗi, wanda aka gudanar da gangan. Ya ku matan aure, ku daina kashe mazajen ku saboda sun ci amanar ku.”

Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa yayin da ake yi wa Motunrayo tambayoyi, ta bayyana cewa sun samu sa’insa ne da mijin na ta saboda yaƙi korar wata mai aiki.

Majiyar ta ce Motunrayo ta bayyana cewa a yayin faɗan na su ne ta yi amfani da dutsen-guga mai zafi wajen ƙona ƙirjin mijin ta.

Majiyar ta ƙara da cewa:

“Bayan taƙaddamar ta faru a ranar Lahadi, mijin ta da ƙanin ta sun bar gida domin zuwa mashaya hutawa kafin su dawo gida da daddare. A lokacin da ya dawo, ta ce sunyi hira sosai kafin su kwanta barci.

“A cewarta, ta ba maigidan nata shawarar ya sanya magani a ƙirjin sa, amma sai ya ƙada baki ya ce kada ta damu ɗan ƙaramin ciwo ne zai warke da kansa.

“Ta bayyana yadda suke cikin raha washegari, kawai sai mijin na ta ya fara yin haki yana numfashi dakyar. Sun yi gaggawar zarcewa da shi asibiti inda ya cika. Ba ta faɗa cewa ta ba mijin nata kayan maye ba.

“Mun kuma ji labarin da yake yawo cewa mijin ta ya ɗirka wa wata ciki wanda hakan ya janyo hayaniya a tsakanin su. Sai dai har yanzu muna kan gudanar da bincike.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, Ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa an damƙe Motunrayo da wasu mutane 3 da ake zargin su na da hannu a aikata laifin.

Kamar yadda ya shaida:

“An ajiye gawar sa a ma’adanar gawa da ke asibitin Yaba domin gudanar da bincike. An damƙe matar mamacin da wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a kisan”

Wata mata ta sha dakyar bayan dan da ta haifa yayi kokarin kashe ta da wuka

Wata mata ta kusa rasa ranta bayan dan da ta haifa ya kai mata hari da wuka yana shirin kashe ta.

Matashin saurayin dan asalin jihar Imo ya shiga hannun ‘yan sandan jihar, kan zargin shi da ake na cakawa mahaifiyarshi wuka a wurare daban-daban a mahaifar shi Owerri, a safiyar ranar Litinin 24 ga watan Janairu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe