36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Mutane sun dauka cewa na haukace ne – Cewar hazikin matashi da ya kera mota da kayan da yake tsintowa a bola

LabaraiMutane sun dauka cewa na haukace ne - Cewar hazikin matashi da ya kera mota da kayan da yake tsintowa a bola
  • Wani matashi dan Najeriya mai shekaru 21, Amalu Chikamso, ya kera motar motsa jiki da ke aiki da injina mai sarrafa kansa
  • Mutune da dama sun dauka na haukace ne lokacin da na ke bi bola bola ina tsintan kayan aiki
  • Chikamso ya bayyana cewa yana so ya cigaba da karatu domin ya kara samun gogewa a harkar kere kere

Wani matashi da akai ta yadawa a yanar gizo bayan ya kera mota ya ce mutane da yawa sun dauka na haukace ne. A wata hira da BBC Pidgin ta yi da shi, Amalu Chikamso ya ce a lokacin da ya fara kokarin kera wannan mota, ya kan yi yawo da ga wannan bola zuwa waccan domin neman kayan aiki. Hakan ya sa mutane su ke ganin kamar baya cikin hayyacin sa.

Ina bin bola don neman kayan aiki

Ya kara da cewa tsabar bin bola, babu bolar da ban sani ba a garin Enugu yawo na ke yi tun safe har dare.

Matashin ya kara da cewa tun yana yaro ya ke mafarkin kera motarsa har yakan hada motar wasan yara da robobi.

Chikamso ya kara da cewa, a duk lokacin da zai je makaranta, ya kan dan tsaya a wata bola ya tsinci kayan aiki saboda babu wanda ya taba tallafa masa.

Injin din dana fara hadawa na farko bugawa ya yi

“Dana fara girma sai na fara mafarkin ganin na kera wani abu. A shekarar 2013, ne na kera samfur din helikwafta.

Lokacin da ya fara kera motarsa, Sai ya sa mata injin din motar Golf a cikinta wanda bai jima ba kawai sai ya buga. Ya gagara neman wani injin din saboda rashin kudi.

A yanzu motar da nake kerawa injin din ta “Automatic ne” yana sarrafa kan shi, inda na sawa injin din suna Gravity X saboda na kerata ta yadda ko da ta yi hadari, motar ba za ta jikkata ba.

Ina da burin cigaba da karatu saboda kera wannan motar ya dauke ni watanni masu tsayi wata na 10, har ta kai ga akwai wani lokaci da takaici ya sa naji kamar na hakura da aikin gaba daya.

Ya ce har yanzu yana da sha’awar komawa makaranta ba don kawai ya samu kwalin shedar karatu ba, sai dai don ya kara samun gogewa a harkar kere-kere.

Abinda mutane ke cewa kan wannan hazikin matashi

‘Yan Najeriya da dama sun yi ta sharhi akan wannan hazikin matashi, inda suke cewa:

Enjoyment_daddy1 ya ce:

“Najeriya ma tana da masu hazaka sosai sai dai ba bu masu tallafawa.”

Ms__amarachi ta ce:

“Yana da kaifin basira sosai, ya kamata ya karanci fannin kere-kere.

Janarstriker ya ce:

“A bara a watan Disamba a Yaba na taba ganin shi kawai ban samu lokacin yin bidiyonsa na yada a yanar gizo ba ne.”

Fiifi_guidance ta ce:

“Ooohhhh Afrika, wanan yaron ai kadara ce amma rashin tallafi zai sa ya zama abin banza.

Hadi Usman dattijo mai shekaru 67 da ya kirkiro murhu mai amfani da ruwa da baya bukatar gas ko kalanzir

Wani hazikin dattijo dan Najeriya da ke zaune a unguwar Jeka da fari da ke jihar Gombe ya kawowa jama’a sauki inda ya yi kokarin kirkirar sabon samfurin murhun dafa abinci, wanda ya ke amfani da ruwa, Hadi Usman mai shekara 67 da haihuwa, ya kirkiri murhun girki wanda baya bukatar amfani da gas ko kalanzir wajen kunna shi.

Dalilin da yasa ya kirkiri wanan murhu mai aiki da ruwa

Kamfanin dillancin labarai na PR Nigeria ya ruwaito cewa, dattijon wanda yake makeri ne ya kirkiro wanan fasaha ne saboda burinsa na son bayar da tallafin wajen ganin an samu saukin rayuwa.

Wani faifan bidiyo na YouTube wanda kafafen yada labarai suka yada ya nuna yanda Malam Hadi Usman yake bayani kan yadda ake amfani da murhun.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe