24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Gimbiya Diana ta yi niyyar shiga addinin Musulunci Allah bai yi ba har ta koma ga Allah – Dan jaridar masarautar Ingila

LabaraiGimbiya Diana ta yi niyyar shiga addinin Musulunci Allah bai yi ba har ta koma ga Allah - Dan jaridar masarautar Ingila

-Gimbiya Diana ta yi sha’awar shiga Muslunci a dalilin wani masoyinta dan kasar Pakistan
-Sun shafe zamani mai tsawo suna tare, wanda har ta kai ziyara ga mahaifansa
-Masoyin nata Dr Hasnat ya bayyana cewa aurensu ba zai yiwu ba saboda banbancin Al’ada

Wani mai daukar hoton cikin Masarautar kasar Birtaniya ya bayyana cewa Marigayiya Gimbiya Diana ta yi kwadayin shiga addinin musulunci a inda ta dinga bi tana neman sani game da addinin Musulnci da kuma neman sani game da mai addinin ya ce akan auren wani mabiyin addini da ban.

Ta nemi wannan sani ne a lokacin da suke tafiya cikin jirgi yayin wani rangadi da za suka je, kimanin shekaru casa’in da suka gabata.

Anwar Hussein shine dan jarida mafi dadewa a gidan Sarautar Ingila

A lokacin, an ba da rahoton cewa gimbiya ta yi ta tambayar Anwar Hussein, mai kimanin shekaru 83, wanda ya kasance ɗan jarida mafi dadewa a kan harkar daukar hoto na gidan sarauta, wanda ya hada tarihin rubutun tafiyar Gimbiya Diana daga shekarar 1980 har zuwa lokacin rasuwarta a shekarar 1997.

Gimbiya Diana ta kasar Ingila
Diana Spencer, Princess of Wales 4

A wannan lokacin, Gimbiya Diana, wacce ta kasance tana bin addinin Kiristanci, ta fara soyayya da wani likitan zuciya Musulmi mai suna Dr Hasnat Khan. Kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito, cewa Gimbiyar ta fara tunanin shiga addinin Musulunci domin ganin ta mallaki masoyinta sunyi aure.

Anwar ya ce Gimbiya Diana ta same shi don suyi wata magana

A wata hira da ya yi da mujallar People Magazine, Hussein ya ce ya tuna lokacin da gimbiya ta zo ta sameshi akan ta na so su dan yi wata magana.

Abinda yasa ta tunkareshi da wannan maganar saboda tasan cewa ya na auren wata Baturiya mai suna Caroline. Shi yasa ta ke son sanin me ye addinin Musulunci ya kunsa musamman inda akayi bayanin auren wani addini daban.

Ba tare da da ta fito fili ta bayyana min dangantakarta da masoyinta Dokta Hasnat ba ita a tunaninta na sani, inda yake tunanin a wannan lokacin tana shakkun yadda dangin ta zasu dauki maganar.

Gimbiya Diana naa matukar son masoyinta – Jemima Khan

A shekarar 2013, wata kawar Diana, mai suna Jemima Khan, wanda su kayi tafiya rangadi zuwa Pakistan tare a shekarar 1996, ta ce gimbiya Diana tana matukar son Hasnat. Har ta taba kai wa danginsa ziyara a lokacin data je Pakistan a inda ta fara tunanin komawa Pakistan don kasancewa tare da masoyinta.

Amma kash hakan bai yiwu ba domin kuwa masoyinta Hasnat Khan ya fito ya bayyana mata cewa fa aurensu ba abu bane mai yiwuwa. Mahaifinsa, Abdul Rasheed Khan, ya ce dan na sa ya shaida wa ’yan uwan sa cewa idan ya auri Gimbiya Diana to fa auren na su ba zai je ko ina ba saboda a’ladunsu da ya banbanta.

Gimbiya Diana ta rasu ne a shekarar 1997 a wani hatsarin mota da ya rutsa da ita tare da wani masoyinta mai shirya fina-finai mai suna Dodi Al-fayed wanda sukayi soyayya na wasu watanni, wanda shi ma Musulmi ne.

Uroosa Arshid – ‘Yar aikin kwana-kwana ta farko da ta fara sanya Hijabi a Birtaniya

Wata budurwa ‘yar shekara 27 a duniya mai suna Uroosa Arshid, an bayyana cewa ta zama mace ta farko ‘yar aikin kashe gobara da ta fara sanya Hijabi. Arshid ta ce babban burinta a rayuwa shine ta zama ‘yar aikin kwana-kwana duk da kuwa mutane na kushe aikin.

A wata hira da aka yi da ita, Arshid ta ce ta tuna lokacin da take makaranta, a lokacin bata wuce shekara 8 ba a duniya, wasu ‘yan aikin kashe gobara uku suka je makarantar ta, tun daga lokacin taji tana sha’awar aikin.

Ta kara da cewa ‘yan aikin kwana-kwana na daya daga cikin mutanen da suka fi kowa ceton al’umma, hakan ya sanya ta shiga wannan aiki. Babban burinta shine ta ga tana taimakawa mutane, da kuma kare rayukan mutane.

Kimanin shekaru biyu da suka gabata, Arshid ta shiga aikin kwana-kwana a ma’aikatar kashe gobara ta Nottinghamshire.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe