36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Kotu ta bada umarnin a izo keyar tsohuwar ministar man fetur, Alison-Madueke a duk inda take a duniya

LabaraiKotu ta bada umarnin a izo keyar tsohuwar ministar man fetur, Alison-Madueke a duk inda take a duniya

Mai sharia Bolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya dake Abuja, ya fitar da takarda izinin kamu akan tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke, wadda aka hakikance cewa a kasar Birtaniya take zaune.

Mai shari’a Olajuwon din ya bayar da takaddar ne bayan shigar da rokon nemanta daga mai bada shawara da jagoranci na hukumar yaki da laifukan cin hanci da rashawa EFCC, Farouq Abdullah.

Kotun ta fitarwa da hukumar yaki da laifukan cin hanci da rashawa ranar 3 ga watan Nuwambar shekara ta 2021, da su bada rahoton izo keyar Alison-Madueke din zuwa Najeriya domin ta fuskanci sharia, kuma domin yiwuwar fara sauraren tuhumar ta, amma da ranar da aka sanya sauraren karar tazo, ba aga duriyar EFCC ba balle kuma ita Alison-Madueke din, inda aka ajiye shariar.

An sanya ranar 24 ga watan Janairu don karbar rahoto

Daga nan sai mai sharia ya sake sanya ashirin da hudu 24 ga watan Janairu, domin karbar rahoton ko kuma sauraren jawabin gabatar da karar.

Saboda haka, da aka kira akan lamarin a ranar 24, Abdullah din yana kotun, inda ya shaidawa kotun cewa duk wani kokarin izo keyar Alison-Madueke din da suka yi, tun a lokacin da lamarin yake gaban alkalin da ya gabata mai suna Ojukwu, ya ci tura.

Diezani Alison Madueke
ADDIS ABABA/ETHIOPIA, 09-11 MAY 2012 – Diezani K. Alison-Madueke, Minister of Petroleum Resources of Nigeria, captured during the Ending Energy Poverty Session at the World Economic Forum on Africa held in Addis Ababa, Ethiopia, 9-11 May, 2012.

A fadarsa yace sammacin da shi mai sharia Ojukwu ya fitar akan wacce ake karar, bai yi karfin da za’a iya izo keyarta ba.

Abdullah din, wanda da baki ya nemi takaddar neman kamun, yace, neman izinin yana daga cikin abin da ofishin babban mai sharia na kasa (Attorney General of Nigeria ) bangaren kulada ingizo keyar masu laifi, suke bukata.

Ya kara da cewa, ana da bukatar takaddar neman kamun, saboda yin hakan zai baiwa yan sandan kasa da kasa zimmar tiso keyar wadda ake karar zuwa Nageriya, domin ta amsa tuhumar da ake yi a kanta.

Alkali ya dage sauraren kara har zuwa lokacin da za a gurfanar da Madueke

Mai sharia Olajuwon, din ya sahale takaddar kamun kuma ya dage sauraren lamarin, har sai sanda aka kamo Alison-Madueke din aka gurfanar da ita gaban kotu.

Za’a iya tunawa mai sharia Ojukwun, a ranar 28 ga watan Oktoban shekara ta 2020, yaki yarda da rokon hukumar EFCC din, kan ya fitar da takarda izinin kamu akan Alison-Madueke din, inda ya nuna gazawar hukumar wajen tursasa wa wadda ake zargin, karbar sammacin kotu na baya, wanda kotun ta fitar akan tsohuwar ministar, tun a ranar 20 ga watan Yuli 2020, inda yace izinin kotu baya tashi a banza.

Matatar mai ta Dangote zata fara aiki a cikin wannan shekara ta 2022

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, yace, aikin matatar man fetur ta Dangote da takin zamani, zasu kammala kafin karshen shekarar nan da muke ciki.

Ya bayyana hakan ne yayin da shugaban bankin cigaban Africa, Dr. Akinwumi Adesina, ya jagoranci ayarin wakilcin bankin, zuwa wurin matatar a garin Legas.

Matatar zata fara aikine a karshen zangon karshe na wannan sabuwar shekarar ta 2022.

“Kusan mun kammala duk wani aikin sanya injina, amma yanzu mun fara gwajin duk wani abun daya shafi bangaren ruwane inda shima Kusan Kashi saba’in 70% ya kammala. Abin da muke fata shine, wajen zangon karshe na wannan sabuwar shekarar, zata fara aiki” Inji Dangote.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe