34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Saurayi ya yaudari budurwarsa bayan ta bashi kodar ta guda 1 an dasa ya samu sauki

LabaraiSaurayi ya yaudari budurwarsa bayan ta bashi kodar ta guda 1 an dasa ya samu sauki

Colleen Le budurwa ‘yar shekara 30, wadda take zaune a kasar Amurka, ta bayyana cewa saurayinta a wani lokaci a baya ya bukaci ayi masa dashen koda, saboda yana fama da ciwon koda mai tsanani, wanda ya sanya ake yi masa wankin kodar yana dan shekara 17.

Ta amince ta sadaukar masa da warin kodarta bayan likitoci sun tabbatar da cewa zata yi daidai da ta shi. Bayan an gama aikin ya samu lafiya, ‘yan watanni kadan sai ya ci amanarta ya gudu ya barta.

Colleen wacce take tauraruwar tiktok, ta sami dumbin masu sharhi a kan bidiyon ta da ta wallafa, wanda ta nuna jerin abubuwan rashin kyautawa da yayi mata, inda da yawa suka dinga yaba mata saboda ceto ransa da tayi kuma suna nuna ma bata dace da shi ba.

A bidiyon ta na farko, Colleen ta bayyana cewa tsohon saurayinta ya gaya mata cewa kodarsa tana aiki ne kasa da kashi biyar cikin dari.

Colleen Le, budurwar da ta bayar da kodar ta ga saurayi
Colleen Le, budurwar da ta bayar da kodar ta ga saurayi

Colleen ta ce:

“Sai nayi shawara ko a gwada tawa a gani ko zasu dace da tasa, saboda bana so naga ya mutu, duk na rude.”

Da aka gano cewa zasu dace sai Colleen taci gaba da shirye shiryen bashi kodar, inda aka yi musu aikin a cikin nasara har suka sami lafiya. Sannan a bidiyo na biyun, sai tayi bayanin cewa dangantakar su tana cikin garari.

Bayan wata bakwai, sai saurayin nata ya ce da ita zai je wani bikin neman aure shida wani ayari a cocinsu, a can Vegas, a karshen mako.

Colleen tace, ita ba wai tafiyar ce ta dameta ba, saboda ta San shi kirista ne, saboda haka ta ci gaba da shirye shiryen ta na fuskantar jarrabawarta ta karshen a makaranta.

Tauraruwar tiktok din tarasa abin cewa, yayin da saurayin nata ya shaida mata cewa ya ci amanarta yayin da yayi wannan tafiyar.

Colleen tace:

“Bayan an danyi rigingimu.. daga baya sai na yafe masa, sannan na kara bashi wata damar.”

“Bayan wata uku, kawai sai yace ya kawo karshen alakar mu, yace wai ‘idan har haduwar mu ta Allah ce, to zai sake hada mu nan gaba’. Inda ya ci gaba da cire ni a shafukansa na yanar gizo.

Tayi ta yada rashin juriyarta ga cin amanar da yayi mata a cikin bidiyoyi daban-daban, wanda a ciki hadda wanda yace ‘ta bayar da kodarta ne ba dan shi ba, sai domin tana so ta kara kyau’ .

Sakon bidiyon ya sami yawan masu kallo kimanin miliyan biyu 2,000,000, inda da yawa suka dinga Allah wadai da halayyar tsohon saurayin Colleen din da aka yiwa dashen koda.

Kadan daga cikin abubuwan da mutane ke cewa

‘Ina shakka idan ya san girman wani ya baka kodarsa. Ka gindayar da rayuwar kafa kenan, domin rayuwar wani. Gaskiya kina da tsarkin zuciya’.

Maria Levya

‘Karki damu yan mata, dole rayuwarsa ta ta’allaka da taki, kuma dole radadin hakan ya dinga tabashi, har tsawon rayuwarsa’.

issa

‘Baki cancanceshi ba, haka shima bai cancanci ki bashi koda ba’.

foreverdreamer27

‘ kiyi alfahari da kanki, kasantuwar kin ceci ran wani, shine yafi komai.’

bryanmurguia

Ango ya saki amaryar sa a wajen walimar bikinsu kan wata waka da ta saka wacce bata yi masa dadi ba

Wani sabon ango ya saki amaryarsa a wajen bikinsu, bayan ta bukaci da a sanya musu wata waka domin su cashe a wajen bikin aurensu wanda hakan ya jawo cece-ku-ce tsakanin dangin ango dana amarya.

An bayyana cewa shine aure mafi gajarta da aka taba yi a kasar

Ma’auratan sun kafa tarihi wanda auresu ya zamo aure mafi gajerta wanda aka rabu baran baran sakamakon musayar baki da ya afku a lokacin shagalin bikin wanda aka yi a birnin Bagadaza.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe