34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Hadi Usman dattijo mai shekaru 67 da ya kirkiro murhu mai amfani da ruwa da baya bukatar gas ko kalanzir

LabaraiHadi Usman dattijo mai shekaru 67 da ya kirkiro murhu mai amfani da ruwa da baya bukatar gas ko kalanzir
  • Wani dan Najeriya mai shekaru 67 ya kirkiro wani murhu mai amfani da ruwa wanda baya bukatar gas ko kalanzir wajen amfani
  • Wannan hadadden murhu yana amfani da ruwa da iska ne wanda hakan yake taimaka wa wajen kamawar wutan wanan abu ne mai ban mamaki
  • Mutumin yana neman goyon bayan cibiyoyi domin ganin wanan abu ya habaka a yayin da ake tsaka da damuwar hauhawan farashin gas din girki

Wani hazikin dattijo dan Najeriya da ke zaune a unguwar Jeka da fari da ke jihar Gombe ya kawowa jama’a sauki inda ya yi kokarin kirkirar sabon samfurin murhun dafa abinci, wanda ya ke amfani da ruwa, Hadi Usman mai shekara 67 da haihuwa, ya kirkiri murhun girki wanda baya bukatar amfani da gas ko kalanzir wajen kunna shi.

Dalilin da yasa ya kirkiri wanan murhu mai aiki da ruwa

Kamfanin dillancin labarai na PR Nigeria ya ruwaito cewa, dattijon wanda yake makeri ne ya kirkiro wanan fasaha ne saboda burinsa na son bayar da tallafin wajen ganin an samu saukin rayuwa.

Wani faifan bidiyo na YouTube wanda kafafen yada labarai suka yada ya nuna yanda Malam Hadi Usman yake bayani kan yadda ake amfani da murhun.

A baya har karamin gidan rediyo ya bude

Mutumin ya kasance mai hazaka wanda a baya ya taba hada na’urar watsa shirye-shirye tare da bude dan karamin gidan rediyon a cikin unguwar su yana rokon cibiyoyi masu fada aji da su taimaka masa aikinsa ya samu karbuwa.

Har ila yau yana so ya samu hadin gwuiwa da manya wajen ganin an samar da shi da yawa.

“Ina fatan cibiyoyi da hukumomin da abin ya shafa za su ba da goyon baya don ganin an kera wanan abu da yawan gaske don samar da su isassu wajen ganin an saukaka wa jama’a ba sai sun sayi kalanzir ko gas ba wajen dafa abincin su sai dai kawai suyi amfani da ruwa,” in ji Hadi.

Allah mai iko lallai wanan tsoho yayi bajinta ya kuma yi abinda ba wai a Najeriya ba duniya gaba da ya zasu amfani da wanan baiwa ta shi.

Hadi Usman dattijo da ya kirkiri murhu
Hadi Usman dattijo da ya kirkiri murhu

A baya in ba a manta ba Jaridar Labarun Hausa ta kawo muku rahoton yanda gwamnatin tarayya ke kokarin cire talafin man fetur, wanda hakan zai kara hauhawar farashin man fetir a fadin Najeriya.

Idan kuwa wannan tsoho ya samu tallafi aka kirkiri wannan murhu da yawa to fa za a samo sauki da ga matsananciyar tsadar rayuwa da ake ciki, kuma idan irin wadannan mutane masu baiwa suna samun tallafi daga gwamnati ko wasu mutane daban to fa Najeriya za ta zama kasa abar alfahari.

An karrama Injiniya musulma, Dana Al-Sulaiman da ta ƙirƙiro na’urar gano cutar Daji

An karrama injiniya Musulma don ilimin ta na ƙirƙirar chip wanda ke iya gano nau’ikan cuta daji daban-daban a cikin jikin majinyacin, injiniyan Saudiyya Dana Al-Sulaiman ta sami lambar yabo ta “Innovators Under 35”.

A wata hira da tashar Alekhbariya, Injiniya Dana ta bayyana cewa, na’urar waccce aka yi da ƙananan allura da aka lulluɓe da wani abu sannan aka sanya shi a cikin fata, ya na da iya ɗaukar ruwa, da kuma gano kwayoyin cutar kansa ta hanya mai sauƙi kuma ba tare da lalata ba.

Wata ‘yar asalin kasar Saudiyya, wacce ke aiki a matsayin mataimakiyar farfesa a fannin Kimiyyar Materials da Biotechnology a KAUST ta kara da cewa, dalilin da ya sa ta samar da wannan ci gaba na kirkire-kirkire shi ne yadda al’adar ta rika daukar samfurin marasa lafiya.

Al-Sulaiman ta yi nuni da cewa, na’urar da ta ƙirƙira na iya bayyana nau’ikan cutar kansa, kuma ta na adana makamashi da kudi da lokaci mai yawa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe