34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ango ya saki amaryar sa a wajen walimar bikinsu kan wata waka da ta saka wacce bata yi masa dadi ba

LabaraiAngo ya saki amaryar sa a wajen walimar bikinsu kan wata waka da ta saka wacce bata yi masa dadi ba

Wani sabon ango ya saki amaryarsa a wajen bikinsu, bayan ta bukaci da a sanya musu wata waka domin su cashe a wajen bikin aurensu wanda hakan ya jawo cece-ku-ce tsakanin dangin ango dana amarya.

An bayyana cewa shine aure mafi gajarta da aka taba yi a kasar

Ma’auratan sun kafa tarihi wanda auresu ya zamo aure mafi gajerta wanda aka rabu baran baran sakamakon musayar baki da ya afku a lokacin shagalin bikin wanda aka yi a birnin Bagadaza.

Rahotannin da jaridar yanar gizo ta kasar Birtaniya Mirror ta ruwaito sun bayyana cewa, matar ta bukaci a sanya musu wata wakar wani mawaki dan kasar Syria Mesaytara ta Lamis Kan, mai taken ni ne mai iko dole in mallake ka.

Wasu baitoci daga cikin wakar da suka fusata dangin angon har ta kai ga raba auren

“Ni ne mai iko; kuma zan shimfida mulki san raina sai abinda na ce, zan birkita ma kwakwalwa idan ka daga ido ka kalli ‘yan mata a waje.

“Tabbas, nine mai iko, kai ne guntun sukari na. Muddin muna tare to fa dole ka zama karkashin ikona, za ka kasance karkashin umarnina.”

Ango da amarya
Ango ya saki amaryar sa a wajen walimar bikinsu kan wata waka da ta saka wacce bata yi masa dadi ba ( Image: Getty Images/Image Source)

An bayyana cewa amaryar chashewar ta kawai ta ke ta na bin wakar tana rerawa cikin nishadi da jin dadin, amma sai dai hakan bai yiwa dangin ango dadi ba wanda hakan ne ya haifar da cece-kuce tsakanin dangin guda biyu.

Irin wannan lamari ya taba faruwa a kasar Jordan

Wannan ba, shi ne karon farko da hakan ta faru ba, kuma duka a waka daya ne matsalar ta ke afkuwa, na biyun ya faru ne a ƙasar Jordan a shekarar 2021 da ta gabata.

Mutuwar Aure abu ne da ke faruwa ba zato ba tsammani. Ansha jin labarun mutuwan aure a wurare daban daban musamma anan gida Najeriya, amma zai yi wuya idan mai karatu ya taba jin aure ya mutu saboda waka a Najeriya.

A nan gida Najeria hakan yana faruwa ace ranar daurin aure an fasa amma fa yawanci irin hakan na faruwa ne a bisa dalilai masu karfi, mutuwar aure abun bakin ciki ne to amma idan hakan ya afku ba bu tsimi ba dabara sai dai zubawa sarautar Allah ido.

Ango ya saki Amaryar shi a wajen daurin aure, bayan an aika masa da hotunan tsiraicinta

An daura auren da aka rabu a wajen daurin aure sakamakon halayen banza da amaryar take da su a baya. Ma’auratan na cikin farin ciki da annushuwa a wajen bikinsu, sai aka bawa angon kyautar fure dauke da wani boyayyen sako.

An aika masa da takarda dauke da rubutu a jikin furen

Rubutun dake jikin takardar ya sanya mijin ya fara zargin halayen amaryar tashi, hakan ya sanya shi duba wasu hotuna da aka aiko masa da su.

Angon ya duba hotunan a wani kebantaccen daki

Wannan hotuna dai tsohon saurayin amaryar shi ne ya aiko masa da su, inda da yawa daga cikinsu na tsiraici ne.

Hotunan sunyi muni matuka, hakan ya sanya angon fushi sosai, inda a wajen ya yanke shawarar kawo karshen auren na su baki daya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe