24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matatar mai ta Dangote zata fara aiki a cikin wannan shekara ta 2022

LabaraiMatatar mai ta Dangote zata fara aiki a cikin wannan shekara ta 2022

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, yace, aikin matatar man fetur ta Dangote da takin zamani, zasu kammala kafin karshen shekarar nan da muke ciki.

Ya bayyana hakan ne yayin da shugaban bankin cigaban Africa, Dr. Akinwumi Adesina, ya jagoranci ayarin wakilcin bankin, zuwa wurin matatar a garin Legas.

Matatar zata fara aikine a karshen zangon karshe na wannan sabuwar shekarar ta 2022.

“Kusan mun kammala duk wani aikin sanya injina, amma yanzu mun fara gwajin duk wani abun daya shafi bangaren ruwane inda shima Kusan Kashi saba’in 70% ya kammala. Abin da muke fata shine, wajen zangon karshe na wannan sabuwar shekarar, zata fara aiki” Inji Dangote.

Babban daraktan zartarwa a bangaren tsare-tsare, bunkasa jari, da kuma manyan ayyuka, na rukunin masana’antun Dangote, Devakumar Edwin, yace, matatar mai hadakar bangarori da suka hada da: masarrafar man fetur, masarrafar takin zamani, da kuma aikin dashen bututun karkashin kasa ; wani gagarumin aikin ginin matatar mai ne a duniya baki daya.

Edwin ya bayyana cewa, tace man fetur mai yawan kimanin ganga 650,000 ba karamin canji zai kawo ga tattalin arzikin Nageriya ba.

A fadar sa, yace matatar man ta Dangote zata iya gamsar da bukatun yan Nageriya dari-bisa-dari 100% ta fannin duk wani abin da ya shafi dangin mai, kamar (man fetur, gas, kalanzir da kuma man jirgin sama) har ma a sami ragowa domin fitarwa kasashen waje.

Aliko Dangote
Aliko Dangote

Yace wannan zai iya samar da kasuwa da zata iya kawo tsantsar riba harta kimanin dala biliyan goma sha daya ($11b) a shekara, ga albarkatun dayen mai na Nageriya. Kuma ya bada dala biliyan tara $9b na kudaden kasar waje.

Ya kara da cewa;

“Mun samar da guraben aikinyi ga ma’aikata kimanin 3,580, a bangaren. Banda ma ma’aikatan da yankwangila da yaransu suka dauka a bangaren” Yayi karin haske.

Da yake yabawa Dangote, shugaban bankin cigaban Africa, Akinwumi Adesina yace;

“Abu guda da nafi yabawa ga Alhaji Aliko Dangote, shine, ya meka yardarsa kacokan ga Nageriya, kuma yana narka jarinsa mai nauyi a Africa. Babu wanda zai iya narka irin wannan jarin biliyoyin dalolin dake anan, sai dai idan mutumin ba burin cigaba ne kadai dashiba, a’a har ma da burin a dama dashi wajen ciyar da kasarsa gaba. Lallai muna alfahari da kai da kuma kulawarka ga nahiyar Africa.

“Kusan ma gigicewa nayi, da irin abin da na gani anan yau. Ba kuwa mafarki nake yi ba. Wannan aiki zai dawowa da kasa abin da take kashewa na cinikayya da kasashen waje. Idan ka duba nawa muke kashewa wajen shigo da kaya daga ketare, ya kai kimanin dala biliyan hamsin da bakwai $57b na duka kayan da ake shigo dasu, mu kuma muna kuma fitar da kayan kimanin dala biliyan hamsin da digo hudu ne $5.4b.

“Saboda haka dole mu cike wancan gibin kimanin dala biliyan bakwai din $7b, idan akayi maganarsu anan ya nuna zasu samar da kasuwar gida wadda zata samar da kimanin dala biliyan goma sha daya $11b, kuma wannan ai babbar kasuwa ce, wadda zata adanawa Nageriya kimanin dala biliyan tara $9b a shekara, wajen shigo da da albarkatun danyen man fetur. Saboda haka, wannan babbar ribace ga Nageriya, kai harma ga nahiyar Africa.”

Buhari bai bawa kowa umarnin cire tallafin man fetur ba – Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari babu wanda ya gayawa cewa za’a cire tallafin man fetur.

Ahmad Lawan din yace, shugaban kasar ya fada masa hakan ne yayin da ya kai masa ziyara, ranar Talata 18 ga watan Janairu, domin ya shaida masa damuwar yan Nageriya, akan jita-jitar cire tallafin man fetur din

Ministar kudi Hajiya Zainab Ahmad ce ta fada a watan Oktoban shekarar da ta gabata 2021, cewa gwamnatin tarayya tayi tanadin bada tallafin man fetur dinne kadai, a cikin watanni shidan farko a cikin Wannan sabuwar shekara.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai umarci kowa ba a cikin gwamnatin sa, da ya aiwatar da cire tallafin man fetur.

Daily Trust, sun ruwaito cewa, Lawan din ya fadi hakanne bayan ganawa da shugaban kasar, a gidan gwamnati ranar Talata 18 ga watan Janairu a Abuja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe