27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

An ceto mutum 2,155 da masu garkuwa suka sace a Zamfara a cikin wata hudu

LabaraiAn ceto mutum 2,155 da masu garkuwa suka sace a Zamfara a cikin wata hudu

Gwamnatin jihar Zamfara tace ta tseratar da mutane 2,155 wadanda yan garkuwa da mutane suka sace a jihar, daga watan Satumba na shekarar 2021 zuwa watan Janairun wannan shekara ta 2022.

Kwamashinan yada Labarun jihar Ibrahim Dosara, shine ya bayyana hakan a garin Gusau a ranar Lahadi 23 ga watan Janairu, inda yace, an samu nasarar ne sakamakon hadin kai tsakanin jami’an tsaron da aka girke a fadin jihar.

Wadanda aka tseratar da suka hada da ‘yan makaranta, daliban firamare, mata da kuma kananan yara, tuni an sada su da ‘yan’uwan su.

“Muna nuna godiyar mu ga jami’an tsaro, saboda rubanya kokarin su a ‘yan kwanakin nan “

“Ayyukan jami’an tsaro daban-daban, na bayannan wanda sukayi a dajin Gando, ya tarwatsa yan ta’addan da suke a wurare daban-daban, kuma ya kassara karfin da suke dashi.

“Kawo karshen wannan mummunan ta’addanci, za’a iya cewa yazo kusa a irin wannan lokacin, da kuma kyakkyawan fatan da ya dara na kowanne lokaci ” Kwamashinan ya fada.

Ya kara da cewa, Gwamna Bello Matawalle yana aiki tukuru wajen ganin dawowar doka da oda a jihar, duk da kalubalen tsaro da take fuskanta.

Ya kara sanar da cewa Matawallen ya taba bayyanawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, irin matakan da jihar ta dauka, domin fuskantar matsalolin tsaro, wanda suka hada da ganawa da Shugaban kasar Niger, Mohamed Bazoum a jihar Niamey.

Hotunan gwamnonin Arewa tare da rikakken dan bindiga da ya addabi al’umma ya jawo kace nace

Masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun bukaci a gudanar da tsatsauran bincike kan alakar wasu gwamnonin arewa da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji, bayan da hotunansu da wani na hannun daman sa mai suna Musa Kamarawa ya bayyana a shafukan sada zumunta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an ga Kamarawa a cikin hotuna ba adadi tare da gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal tare da kuma mataimakin gwamnan Sokoto, Mannir Dan Iyya.

Jaridar Labaru Hausa ta lura cewa jihohin Zamfara da Sokoto suna daga cikin jihohin Arewa maso yamma da ke fuskantar matsalar tsaro, hare-haren ‘yan bindiga inda aka hallaka daruruwan rayuka tare da raba dubbai da muhallansu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe