24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wata mata ta sha dakyar bayan dan da ta haifa yayi kokarin kashe ta da wuka

LabaraiWata mata ta sha dakyar bayan dan da ta haifa yayi kokarin kashe ta da wuka

Wata mata ta kusa rasa ranta bayan dan da ta haifa ya kai mata hari da wuka yana shirin kashe ta.

Matashin saurayin dan asalin jihar Imo ya shiga hannun ‘yan sandan jihar, kan zargin shi da ake na cakawa mahaifiyarshi wuka a wurare daban-daban a mahaifar shi Owerri, a safiyar ranar Litinin 24 ga watan Janairu.

Wani da lamarin ya faru akan idon shi ya bayyana cewa saurayin ya kira mahaifiyar shi, inda yayi amfani da wannan dama ya dinga caka mata wuka.

A cewar mutumin:

“Mahaifiyar shi na ihu tana neman taimako da jini na fita daga jikinta sakamakon wukar da ya caka mata. Makwabta sun jiyo ihun ta suka garzaya don ceto rayuwar ta. A lokacin da dan yaga mutane na zuwa don ceton mahaifiyar tashi sai ya daina caka mata wukar.

“A wannan lokacin ne matar ta fadi kasa ta fara kuka, inda makwabtan suka cece ta daga wajen dan nata.

“A yanzu da nake magana daku an garzaya da ita zuwa asibiti, don ceto rayuwar ta. ‘Yan sanda kuma tuni sun kama dan nata sun wuce dashi zuwa ofishin su.

A wani bidiyo da yake ta yawo shafukan sadarwa, matar da aka bayyana sunanta da Mrs Mbachu, wacce take aiki a wata Cocin Katolika a garin Owerri, ta yi godiya ga Allah da ya ceto rayuwar ta.

Ta ce:

“Nagode Allah da ya cece ni. Na kuma godewa makwabtana da suka ceto rayuwata. Nagode duk wani wanda ya zo domin ceto rayuwata.

Dan sanda ya harbe yaro har lahira akan ya daukar masa ‘Pure Water’ guda 1

Wani fusataccen dan sanda ya harbe wani yaro har lahira, sakamakon jayayya da suka yi akan ruwan leda, a garin Kabba tsohuwa, dake karamar hukumar kabba/Banu cikin jihar Kogi, a safiyar ranar Asabar.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta hada, lamarin ya janyo gagarumin ganganko daga mutanen da suka fusata, abin da ya sa duk alamuran kasuwanci suka tsaya cak a garin da lamarin ya faru.

Wani shedar gani da ido yace, yaron ne ya dauki ruwan leda kwaya daya daga cikin motar dan sandan ba tare da sanin sa ba.

Halayyar yaron, bata yiwa dan sandan dadi ba, inda katobarar data biyo baya shine, dan sandan ya sauke fishinsa akan yaron, wanda a nan take ya bindige yaron har lahira.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe