34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ba zan bata lokaci ba wajen sanya hannu akan hukuncin kisan da za a yankewa wanda ya kashe Hanifa – Ganduje

LabaraiBa zan bata lokaci ba wajen sanya hannu akan hukuncin kisan da za a yankewa wanda ya kashe Hanifa - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ba zai bata lokaci ba wajen sanya hannu akan hukuncin kisan da za a yankewa Abdulmalik Tanko, idan har kotu ta gama bincike ta kuma bada dama.

Tanko, wanda yake Malamin Makarantar Noble Kids Academy a cikin karamar hukumar Nasarawa cikin Kano, ya bayyana cewa shi ya kashe Hanifa Abubakar, wacce ya sace ta daga gidansu a cikin watan Disambar shekarar 2021.

A ranar Litinin 24 ga watan Janairu, gwamnan yayi alkawarin bin duk wata doka da ta bashi damar sanya hannu don yankewa Tanko hukuncin kisa, matukar kotu ta amince da hakan.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya tare da mataimakin shi, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjaye na majalisar jihar, Labaran Abdul Madari da kuma wasu daga cikin manya na gwamnatin shi, inda suka je gidan iyayen Hanifa dake unguwar Dakata/Kawaji.

“Mun samu tabbaci daga kotu cewa za ta yi iya bakin kokarin wajen zartar da hukuncin da ya dace, za a yi adalci. Duk wanda aka samu da a wannan aika-aika zai fuskanci hukuncin kisa ba tare da bata lokaci ba. A matsayin mu na gwamnati tuni mun fara wannan shirye-shirye.”

“Dokar mu ta bada damar yin hakan, idan aka yankewa mutum hukuncin kisa, doka ta bawa gwamna damar sanya hannu domin yanke hukuncin, kuma nayi muku alkawarin ba zan bata koda dakika daya ba wajen sanya hannu akan hakan.”

Dangane da yadda shari’ar ke tafiya, gwamnan ya bayyana cewa za a yi gaggawar yanke hukuncin, inda ya kara da cewa:

“Gwamnati za ta lura da iyayen diyar mu marigayiya Hanifa domin dinga tunawa da ita.”

Dangane da makarantun da wannan lamari ya shafa, gwamna Ganduje ya yi alkawarin gwamnati za ta dauki mataki akan haka.

Muna goyon bayan hukuncin Malam – Aisha Buhari ta goyi bayan Sheikh Abdallah kan a yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta sanya baki dangane da maganar hukuncin da ya kamata a yankewa Abdulmalik Muhammad Tanko, shugaban makarantar su Hanifa Abubakar, wacce ya sace ta ya kuma yi mata kisan gilla.

Matar shugaban kasar ta bayyana ra’ayinta a shafin ta na Instagram a ranar Litinin 24 ga watan Janairu, inda ta nuna goyon bayan ta akan a kashe Abdulmalik Tanko kamar yadda ya dauki rayuwar Hanifa.

Aisha ta bayyana hakane sakamakon wani bidiyo na Shahararren Malamin addinin Islama din nan na jihar Kano, Sheikh Dr Abdallah Gadon Kaya, wanda ya bukaci a yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa.

Matar shugaban kasar wacce ta wallafa bidiyon Malamin a shafinta, ta yi rubutu a kasa, inda take cewa:

“Muna goyon bayan hukuncin Malam”.

A cikin bidiyon Sheikh Gadon Kaya ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da su sanya a yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa, kamar yadda ya kashe Hanifa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe