27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Babu adalci idan dan Arewa ya cigaba da rike kujerar shugaba Buhari a 2023 – Tanko Yakasai

LabaraiBabu adalci idan dan Arewa ya cigaba da rike kujerar shugaba Buhari a 2023 - Tanko Yakasai

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana ta tafka muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar nan, game da batun karba-karba mulki a tsakanin ‘yan Arewa da ‘yan Kudu, musamman zaben 2023 me gabatowa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal; da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, na daga cikin ’yan siyasar Arewa da ke kai ma kujerar Buhari wawura.

Ni dan siyasa ne, amma bani da jam’iyya

Yakasai ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, duk da cewa shi bai da wata jam’iyya da yake goya wa baya, amma shi dan siyasa ne inda ya bayyana cewa hakan ba adalci ba ne ace dan Arewa ya sake maye gurbin Shugaba Buhari a 2023 mai makon dan Kudu.

Ya ce:

“Ya za a yi a kullum mu ’yan Arewa mune akan mulki? Hakan ba adalci ba ne, ya kamata a ce idan munyi mulki, wani zagayen kuma sai a bawa ‘yan kudu mulkin hakan shine adalci.

“Duk da cewa a tsawon shekarun da ’yan Arewa suka yi mulki ba bu wani abun azo a gani da muka yi , me za mu ce wa jama’a? Me za mu fito mu nuna wa ’yan Najeriya wanda zamu kafa hujja da shi na cewa munyi musu aiki domin su sake ba mu kuri’unsu?

Shekaru shida muka yi babu abinda muka tsinana

“A cikin wadannan shekaru shida zuwa bakwai da mukayi mulki me muka yi? Wace nasara muka samu wacce ta taimaka wajen ci gaban kasa, tattalin arzikinta ko wani ci gaban taimakon al’umma? Wace babbar nasara muka samu da za mu yi amfani da ita wajen nuna wa ‘yan Najeriya dom mu kiranyesu su,su sake ba mu kuri’unsu?

“Saboda haka, Ni ra’ayina shi ne, idan wa’adin Muhammadu Buhari ya kare, ya kamata Arewa ta hakura, Buhari ze kare wa’adinsa na shekara takwas, ta yaya za ace kuma wani dan Arewa ne zai maye gurbinsa shi ma yazo yayi shekaru takwas, tunda kowane zangon shekara hudu ne kuma abun kaman an maidashi dole sai dan takara yayi sau biyu .Gaskiya wannan ba adalci bane.

Na so ace kowanne shugaban kasa yayi mulki sau biyu

Ya ci gaba da cewa, sha’awarsa ga siyasa tun farko shine kwatanta adalci, inda ya bayyan ra’ayinsa ga goyon bayan da ya bai wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015, “saboda na so ace kowane shugaban kasa ya yi mulki karo biyu. Kamar yadda na, fada a farko.

“Idan shekaru hudun farko na mulkin ba su ishi shugaban kasa ya karasa ayyukan sa ba, to sai ya zarce shekaru takwas za su ishe shi matukar yana da shiri maikyau kan yadda zai cim ma su.”

Idan ba a manta ba jaridar Labarun Hausa ta ruwaito yanda masu ra’ayin gaje kujerar shugaban cin kasar nan suka kunno kai,a inda kowanne su yake nuna ma duniya cewa idan aka bashi dama fa to za ga ayukan ci gaba da damam da ze yi kokarin kawo su.’Yan takara kamar su Bola Ahmad Tinubu,Ahmad Sani yariman Bakura,Yahya Bello da dai saura su sun fito sun bayyana ra’ayinsu nason samun wanan kujera tare da alkwaruka daban daban.

‘Yan Najeriya za su samu ilimi kyauta da zarar na zama shugaban kasa – Bola Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin biyan kudaden jarrabawar kammala sakandare wato WAEC ga kowane dalibi dan Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta yada a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe