34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ahmed Musa ya nuna takaicinsa kan kisan yarinya ‘yar shekara 5 Hanifa Abubakar a Kano

LabaraiAhmed Musa ya nuna takaicinsa kan kisan yarinya 'yar shekara 5 Hanifa Abubakar a Kano

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, yayi bakin ciki, bayan da ya samu labarin abinda ya faru da Hanifa Abubakar daga kasar Kamaru inda yake wakiltar Najeriya a gasar AFCON ta 2021.

An rawaito cewa kawun mamaciyar, Suraj Suleiman, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ya sace yarinyar ya kai yarinyar ga matarsa ​​wadda ta ki ci gaba da rike ta.

Kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Ahmed Musa ya yi tir da kisan wata yarinya Hanifa Abubakar mai shekaru biyar bayan da aka gano gawar ta a wata makaranta da ke unguwar Tudunwada a jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa, duk da cewa an biya wani kaso na kuɗin fansa na Naira miliyan shida da masu garkuwan suka nema.

Hanifa da wanda ya kasheta
Ahmed Musa ya yi martani kan kisan Hanifa, yarinyar Kano mai shekaru 5

A cewar Daily Nigerian, an sace Hanifa da misalin karfe 5 na yamma a ranar 4 ga watan Disamba yayin da take kan hanyarta ta komawa gida daga makarantar Islamiyya.
An ce masu garkuwa da mutanen sun isa wurin ne a cikin keken kasuwanci guda uku sannan suka lallaba ta domin su hau.
Kawun na ta Suraj Suleiman, ya ce kamar yadda jaridar Information Ng ta ruwaito:

“Mai garkuwa da mutanen ya fara kai Hanifa wurin matar sa, amma matar ta ki rike ta. Daga nan ya kai ta Tudunwada inda yake aiki da wata makarantar kudin sannan ya bata shayi da gubar bera . Bayan an ba ta guba ta mutu, sai masu garkuwa da mutanen suka yanka gawar ta gunduwa-gunduwa suka binne a cikin makarantar.”

Sai dai an damke masu garkuwa da mutane a kusa da titin Zaria a Kano a lokacin da suke yunƙurin karɓar kaso na biyu na kudin fansa.

Lamarin da ya sanya kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa baƙin ciki yayin da dan wasan da ya je kasar Kamaru domin halartar gasar AFCON ya mayar da martani a shafukansa na sada zumunta.

Musa ya sa hoton marigayiya Hanifa a cikin labarin sa na Instagram kuma ya kara da taken “ki huta lafiya Hanifa,” – tare da wasu hotuna guda uku na kuka.

Zan bawa iyayen Hanifa kyautar diya ta Fatima don rage musu radadi – Malaam Abdullahi

Yayin da al’umma ke ci gaba da jimami dangane da wannan lamari na kisan yarinya ‘yar shekara biyar Hanifa da Malamin ta Abdulmalik Tanko ya yi a jihar Kano, wani bawan Allah ya fito ya bayyana kudurin shi na taimakawa iyayen Hanifa domin rage musu radadi.

Mutumin mai suna Malam Abdullahi Ahmed Latus wanda ya fito daga cikin karamar hukumar Darazo dake jihar Bauchi, ya bayyana aniyarsa ta bayar da diyarsa mai suna Fatima kyauta ga iyayen marigayiya Hanifa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe