24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An dora laifin rashin nasarar Najeriya a AFCON kan kiran wayar da Buhari ya yiwa ‘yan kwallon Najeriya

LabaraiAn dora laifin rashin nasarar Najeriya a AFCON kan kiran wayar da Buhari ya yiwa 'yan kwallon Najeriya


Kafin buga wasan a jiya Lahadi ‘yan Najeriya da dama sun yi hasashen cewa Super Eagles za ta iya yin nasara, musamman yadda ‘yan wasan kwallon kafan Tunisia suka kamu da cutar Coronavirus, wanda ya shafi kimanin ‘yan wasa 12 da suka hada da kyaftin, da kuma kocin kungiyar.

A ranar Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana da ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya ta wayar tarho na bidiyo.

Koci Augustine Eguavoen ya ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari tabbacin cewa kungiyar kwallon kafan ba za ta ba wa mara da kunya ba.

Najeriya, wacce ta taka babban rawa a matakin rukuni, amma kash tasha kaye a karonta da tunisia a ranar Lahadi.

‘Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun mayar da martani akan cewa bai kamata shugaban kasa ya kira Super Eagles ba.

Abinda ‘yan Najeriya ke cewa

A Facebook, wani Comrd Babangida Bukari, ya rubuta:

“Buhari Buhari Buhari, me ya sa ka kira su?”

Hussaini Abdulkarim Maikudi, wanda shi ma ma’abocin Facebook ne, ya ce,

“Ai Tun da na ji Buhari ya yi waya da super eagle, na san nasara ta zo karshe.

Idowu Olawale, ya ce,

“Shaho ta ki tashi a filin wasa saboda bubu ya musu kiranye, Bubu ya kira Super Eagles, shaho ya gagara ta shi.”

Yakubu Umar, ya rubuta

“Kira daya daga wannan mutumin komai ya lalace.”

A shafin Twitter, wani Amarachukwu, ya rubuta:

“Ya Ubangiji, ka hanani daukar duk wani kira da zai zamo faduwa a gareni.

Tweeting ta @timiPR, wani ya rubuta,

“Allah ka hanamu daukan kiran da zai canja mana kyakyawan kaddararmu.”

Wani mai abun dariya Violence AspicPrince ya rubuta,

“Ina ji Buhari ya, kira waɗannan yaran, na san cewa wahala don dey #Nigeriavstinisia.”

Reno Omokri ya dora laifin akan Buhari shi ma

Da yake magana a shafin sa na Twitter, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa;

“Iwobi red card, Iheanacho yellow card. Tun farkon fara wasa su hakan bai taɓa faruwa ba. Me ya sa a ranar da suka yi magana da Buhari ne wadannan abubuwan suka afko mana! Karfin abun tsoro ne sosai. Allah kai mana tsari da fara kafa!”

Shahararrun mawaka Davido, da Dremo, sun wallafa a shafinsu na Twitter cewa,

“Buhari me yasa haka.”

Ace disc jockey , DJ Switch, sun wallafa a shafinsa na Twitter cewa,

“Buhari kawai ka ja mana cin da f, f ka bata mana wasanmu. Buhari ga super eagles: “go and make us froud” yanzu gashi mun fadi.”

Yayin da take bayyana ra’ayinta, fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood Beverly Naya itama ta dora laifin kiran da shugaban kasa yayi da rashin nasarar Super Eagles. Ta wallafa a shafinta na twitter;

“Dama ai karshenta, sai dai super eagles su sha kuka. Tunda Buhari ya kira su, nasara ta kwace mana!”.

A baya dai mun samu labarin irin kwazon da ‘yan kwallon kafan Najeriya ta yi a wasan cin kofin nahiyar Afirka inda Super Eagles su kai bajinta sosai har ta kai ga an basu makin jinjina daga kungiya kula da kwallon kafan.Amma kuma a jiya lahadi labari ya, sha banban inda Super Eagles din suna tsaka da cin karensu ba babbaka kawai kasar Tunusia ta lailaye su.

Ahmed Musa ya bada tallafin N600,000 don cigaba da ginin babban Masallacin Garoua na kasar Kamaru

Ahmed Musa wanda yake shine kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, ya bayar da tallafin kudi har Naira dubu dari shida (N600,000) don cigaba da ginin babban Masallacin Garoua na kasar Kamaru, yayin da kungiyar ta Super Eagles ke shirin karawa da kasar Tunisia a wasan zakarun Afrika.

Tsohon dan wasan Premier League din mutum ne mai bin addinin Musulunci, kuma a lokuta da dama yana nuna yadda yake da riko da addini ga masoyan sa domin kara musu karfin guiwa akan kowanne irin addini suka zaba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe