29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Muna goyon bayan hukuncin Malam – Aisha Buhari ta goyi bayan Sheikh Abdallah kan a yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa

LabaraiMuna goyon bayan hukuncin Malam - Aisha Buhari ta goyi bayan Sheikh Abdallah kan a yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta sanya baki dangane da maganar hukuncin da ya kamata a yankewa Abdulmalik Muhammad Tanko, shugaban makarantar su Hanifa Abubakar, wacce ya sace ta ya kuma yi mata kisan gilla.

Matar shugaban kasar ta bayyana ra’ayinta a shafin ta na Instagram a ranar Litinin 24 ga watan Janairu, inda ta nuna goyon bayan ta akan a kashe Abdulmalik Tanko kamar yadda ya dauki rayuwar Hanifa.

Aisha ta bayyana hakane sakamakon wani bidiyo na Shahararren Malamin addinin Islama din nan na jihar Kano, Sheikh Dr Abdallah Gadon Kaya, wanda ya bukaci a yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa.

Matar shugaban kasar wacce ta wallafa bidiyon Malamin a shafinta, ta yi rubutu a kasa, inda take cewa:

“Muna goyon bayan hukuncin Malam”.

A cikin bidiyon Sheikh Gadon Kaya ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da su sanya a yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa, kamar yadda ya kashe Hanifa.

Abdulmalik Tanko ya bayyana hanyoyin da ya bi wajen kashe Hanifa

Idan ba a manta ba jaridar Labarun Hausa ta kawo muku yadda ‘yan Najeriya suka cika da jimami kan kisan Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar da Malamin ta ya kashe.

A bayanin da Abdulmalik Tanko ya yi ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya bayyana cewa ya kashe Hanifa da maganin bera.

Tanko ya bayyana cewa ya siyo maganin bera dinne na naira dari (N100), inda ya yi amfani dashi wajen kashe Hanifa.

Dole sai mun dauki mataki – Gwamnatin Kano ta sha alwashin yin hukunci

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kokari wajen ganin ta hukunta duk wani wanda yake da hannu a wannan aika-aika.

Wannan na fitowa daga bakin Malam Muhammad Garba, Kwamishinan yada labarai na jihar, a wata sanarwa da ya fitar.

Aisha Buhari - Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari
Aisha Buhari – Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari

Gwamnan ya bayyana cewa tuni har an dauki mataki akan wannan lamari, inda aka kwace lasisi da kuma rufe wannan makaranta da aka yiwa Hanifa kisan gilla.

Fusatattun matasa sun kone makarantar Abdulmalik wanda ya kashe Hanifa a Kano

Matasan Irate sun sanyawa makarantar Noble Kids Comprehensive College wuta, wacce ke kan hanyar Warshu Hospital Road, Kawaji Kano, sakamakon kisan Hanifa Abubakar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban makaratar, Abdulmalik Tanko, ya yi garkuwa tare da kuma kashe Hanifa bayan ya karbi kudin fansa daga hannun su iyayenta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe