24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Zan bawa iyayen Hanifa kyautar diya ta Fatima don rage musu radadi – Malaam Abdullahi

LabaraiZan bawa iyayen Hanifa kyautar diya ta Fatima don rage musu radadi - Malaam Abdullahi

Yayin da al’umma ke ci gaba da jimami dangane da wannan lamari na kisan yarinya ‘yar shekara biyar Hanifa da Malamin ta Abdulmalik Tanko ya yi a jihar Kano, wani bawan Allah ya fito ya bayyana kudurin shi na taimakawa iyayen Hanifa domin rage musu radadi.

Mutumin mai suna Malam Abdullahi Ahmed Latus wanda ya fito daga cikin karamar hukumar Darazo dake jihar Bauchi, ya bayyana aniyarsa ta bayar da diyarsa mai suna Fatima kyauta ga iyayen marigayiya Hanifa.

Rahoton da shafin Labari Daga Bauchi na Facebook suka wallafa, Malam Abdullahi, ya bayyana cewa zai bawa iyayen Hanifa kyautar ‘yar tashi ne domin ya rage musu radadin wannan ta’addanci da aka yi musu.

Abdullahi ya ce:

“Na jima ina juyayin wannan al’amari a raina, a ce diya daya tilo da Allah ya basu, rana daya a ce an kasheta, wannan ba karamin abin takaici bane.

Malam Abdullahi ya bayyana cewa wannan abu da ya dauki aniya zai yi ne da zuciya daya, inda har ya bayar da lambar wayarsa, ya ce:

“Har cikin zuciya na wallahi zan basu kyautar fatima in dai sun aminta da hakan.

Abdullahi Ahmed Latus.

08069662069

Mansurah Isah ta fashe da kuka ta roki gwamnati ta yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama’a

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Mansurah Isah ta rushe da kuka kan kisan gillar da Abdulmalik Tanko ya yiwa Hanifa a jihar Kano…

Yayin da al’umma suka zuba ido suna jira su ga irin hukuncin da gwamnati za ta dauka akan Malamin makaranta Abdulmalik Tanko, wanda ya yiwa Hanifa kisan gilla, ta hanyar bata maganin bera ya kuma daddatsa gawarta ya binne, wasu mutane tuni sun fara nuna ra’ayinsu akan irin kisan da ya kamata gwamnati ta yiwa wannan mutumi.

A cikin makon nan ne dai asirin Abdulmalik Tanko ya tonu, bayan ya sace Hanifa ya boye ta a gidan shi tsawon kwanaki 47, daga baya kuma ya kasheta ta bayan ya karbi kudin fansa daga wajen iyayenta.

Mutane da dama sun nuna takaicin su, inda suke hawa shafukan sada zumunta suna Allah wadai da kuma tofin Allah tsine ga wannan rashin imani da Malamin makarantar ya yiwa dalibar ta shi.

A yayin da jaridar Labarun Hausa ke cigaba da bibiyar abubuwan dake wakana, ta gano wani bidiyo na fitacciyar jaruma Mansurah Isah, inda take rusa kuka da nuna takaici kan wannan lamari, inda ta roki gwamnati ta dauki tsattsauran mataki akan wannan azzalumin mutumi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe