35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Fusatattun matasa sun kone makarantar Abdulmalik wanda ya kashe Hanifa a Kano

LabaraiFusatattun matasa sun kone makarantar Abdulmalik wanda ya kashe Hanifa a Kano

Matasan Irate sun sanyawa makarantar Noble Kids Comprehensive College wuta, wacce ke kan hanyar Warshu Hospital Road, Kawaji Kano, sakamakon kisan Hanifa Abubakar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban makaratar, Abdulmalik Tanko, ya yi garkuwa tare da kuma kashe Hanifa bayan ya karbi kudin fansa daga hannun su iyayenta.

An kone makarantar su Hanifa da daddare

Lamarin ya faru da tsakar daren ranar Lahadi 23 ga watan Janairu, 2022, inda a yayin da jaridar Daily Nigerian ke daukar wannan rahoto, wutar na cigaba da ci a makarantar ganga-ganga.

Tuni dai dama gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin kulle makarantar, bayan kama shugaban makarantar Abdulmalik Tanko da kisan Hanifa mai shekaru biyar a duniya.

Akwai maganganu da ake ta yadawa dangane da kisan, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin tabbatar da adalci ga duka wadanda ke hannu a wannan ta’addanci.

Makarantar mutumin da ya kashe Hanifa kenan take ci da wuta
Makarantar mutumin da ya kashe Hanifa kenan take ci da wuta

Abdulmalik dai ya sace Hanifa daga gidansu, inda ya boye ta a gidan shi tsawon kwanaki 47, ya kuma bukaci iyayenta da su biya shi kudin fansa, bayan sun bashi wani bangare na kudin ya bata maganin bera ta mutu, sannan kuma ya daddatsa gawarta ya binne tare da tallafin wani abokin shi.

Da nasan haka zai kasance da ko auren shi ban yi ba, Matar wanda ya yi garkuwa da Hanifa

Matar mutumin da aka ɗamke da laifin yin garkuwa da kuma kisan wata ƙaramar yarinya a Kano, Hanifa Abubakar ta bayyana yadda maigidan na ta ya yaudare ta ya kawo yarinyar gida kafin daga bisani ya halaka ta.

Matar ta bayyana cewa ƙarya mijin na ta ya sharara mata cewa iyayen yarinyar sun yi tafiya, shiyasa su ka damƙa masa amanarta kafin su dawo daga tafiyar da su kayi.

Ta dai bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Dala FM ta ruwaito.

“Cewa yayi mahaifiyar yarinyar tana koyarwa a makarantar sa, ta samu aiki a Saudiyya za ta je birnin tarayya Abuja ta sa hannu, shiyasa ta bashi ajiyar yarinyar kafin ta dawo”

“Ya faɗa min cewa iyayen mahaifiyar Hanifa mazauna Maiduguri ne kuma mijin ta dan kabilar Ibo ne shiyasa ba a kai mu su yarinyar ba sanda na tambaye shi dalilin da yasa matar ta bashi ajiyar yarinyar maimakon ta kai wa ‘yan’uwanta.”

Na yi dana sanin auren mijina

A cewar ta, ta yi dana sanin auren mijin na ta a dalilin wannan ɗanyen aikin da ya aikata.

“Da na san haka zan zo na kasance da ni da yara na da ban aure shi ba” a cewar ta.

A na sa ɓangaren, Abdulmalik Muhammad Tanko wanda ake tuhuma da aikata wannan mummunan aikin na garkuwa da kuma halaka Hanifa, ya bayyana cewa sharrin shedan ne ya rinjaye shi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe