34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Bayan shafe shekaru 12 tana neman haihuwa, wata mata ta haifo ‘yan biyar a Saudiyya

LabaraiBayan shafe shekaru 12 tana neman haihuwa, wata mata ta haifo 'yan biyar a Saudiyya

Wata mata a Saudiyya tayi gamo da katar bayan ta samu ƙaruwa inda ta haifo yara biyar a lokaci guda.

Matar wacce ta kwashe shekaru 12 tana neman haihuwa, ta haifi ‘yan biyar ɗin ne a asibitin sojoji na Sarki Salman da ke a birnin Riyadh da ke Saudiyya. Cikin ikon Allah, dukkanin jariran guda biyar suna cikin ƙoshin lafiya da walwala.

Bayan shafe shekaru 12 tana neman haihuwa, wata mata ta haifo 'yan biyar a Saudiyya
Bayan shafe shekaru 12 tana neman haihuwa, wata mata ta haifo ‘yan biyar a Saudiyya

Hukumomin asibitin da ke Saudiyya sun shaida cewa matar ta shafe watanni 28 ɗauke da juna biyun. Tana cikin ƙoshin lafiya tare da jariranta waɗanda ke da nauyin gram 950 zuwa 1,100.

Matar ta tunkari asibitin a Saudiyya domin a duba ta bayan ta kwashe shakaru 12 ba ta haihu ba. Sai gashi yanzu ta samu ‘yan biyar a lokaci ɗaya.

Mutane da dama sun yaba wa ma’aikatan asibitin a Saudiyya bisa jajircewar su da kwazon da su ka nuna wajen amsar haihuwar.

Wani mutum mai suna Mjahed Alatawi, ya yi tsokaci inda yace:

“Ba mu yi mamakin samun wannan babbar nasara ba daga wajen wannan gagarumar tawagar. Muna rokon Allah ya ba su nasara sannan muna godiya matuƙa ga shugaban asibitin.”

A nasa ɓangaren, Manjo Janar Attia Al-Zaharani, shugaban kula da sashin unguwar zoma da ciwukan mata, ya samu yabawa sosai daga wajen mutane.

An karrama Injiniya musulma a Saudiyya, Dana Al-Sulaiman da ta ƙirƙiro na’urar gano cutar Daji

An karrama injiniya Musulma don ilimin ta na ƙirƙirar chip wanda ke iya gano nau’ikan cuta daji daban-daban a cikin jikin majinyacin, injiniyan Saudiyya Dana Al-Sulaiman ta sami lambar yabo ta “Innovators Under 35”.

A wata hira da tashar Alekhbariya, Injiniya Dana ta bayyana cewa, na’urar waccce aka yi da ƙananan allura da aka lulluɓe da wani abu sannan aka sanya shi a cikin fata, ya na da iya ɗaukar ruwa, da kuma gano kwayoyin cutar kansa ta hanya mai sauƙi kuma ba tare da lalata ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe