35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Labari mai dadi: Bankin duniya ya bawa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 311 ta rabawa talakawan Najeriya

LabaraiLabari mai dadi: Bankin duniya ya bawa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 311 ta rabawa talakawan Najeriya

Gwamnatin shugaba Buhari ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna NG-CARES da naira tiriliyan 311.2 domin farfaɗo da tattalin arzikin kasa

Shirin zai bayar da ƙarfi ne wajen samar da ayyukan yi da tallafa wa masu ƙananun sana’o’i da kuma ɓangaren noma

Gwamnatin shugaba Buhari ta ƙaddamar da wani sabon shirin tallafa wa talakawa
Gwamnatin shugaba Buhari ta ƙaddamar da wani sabon shirin tallafa wa talakawa

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya ƙaddamar da shirin, ya ce shirin zai gudana ne na tsawon shekaru 3 sannan za a rarraba kuɗaɗen ne a tsakanin jihohin ƙasar

Gwamnati za ta karbo bashin tiriliyan 311

A yunƙurin shirin na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, gwamnatin tarayya ta fito da wani sabon shiri mai suna NG-CASES wanda da za a aiwatar da bashin bankin duniya har naira tiriliyan 311,250.

Mataimakin shugaban ƙasa, farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a ranar Alhamis 20 ga watan Janairu, 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

Wani rahoto daga Nairametrics ya bayyana cewa shirin na NG-CARES, shiri ne wanda ya ke da ɓangarori da dama. Shirin zai cigaba da gudana tare da sauran shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci na gwamnatin tarayya da ke gudana a ƙasar.

A cewar farfesa Osinbajo, shirin an yi shi ne domin talakawan ƙasar.

Abinda shirin shugaba Buhari ya ƙunsa

Ya bayyana cewa shirin NG-CARES an tsara shi ne domin tallafawa talakawa, bayar da agajin gaggawa ga ƙananun manoma da masu ƙananun sana’o’i waɗanda annobar cutar korona ta shafa. Ya ƙara da cewa shirin an kafa shi ne akan hanyoyin da ƙasar ta ke bi domin ɗaƙile raɗaɗin da annobar korona ta kawo wa mutane.

Abinda Osinbajo yace

Osinbajo ya ce, bashin na bankin duniya zai shafe tsawon shekaru biyu (2021-2023), kowace jiha za a bata biliyan N8.2, a hasashen da aka yi, babban birnin tarayya Abuja zai samu biliyan N6.2 sannan kowane ɓangaren taimako na shirin NG-CARES zai samu biliyan N6.2.

Na yi alkawarin ba zan ci amanar ‘yan Najeriya ba idan har suka zabe ni shugaban kasa – Yahaya Bello

Gwamann jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yiwa ‘yan Najeriya alkawari cewa ba zai taba cin amanar su ba idan har suka zabe shi shugaban kasa a zabe mai karatowa na shekarar 2023.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnan na jam’iyyar APC shine ya bayyana haka a ranar Alhamis 20 ga watan Janairu, a lokacin wani taro da aka gabatar na yankin Arewa maso Gabas a jihar Bauchi.

Jaridar Labarun Hausa ta gano cewa Yahaya Bello ya bayyana cewa ba zai bawa ‘yan Najeriya kunya ba, saboda shi mutum ne mai cika alkawari.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe