27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Cutar Korona: An haramta wa wadanda ba su yi riga-kafin COVID-19 ba shiga masallatai a Pakistan

LabaraiCutar Korona: An haramta wa wadanda ba su yi riga-kafin COVID-19 ba shiga masallatai a Pakistan

Sakamakon ƙaruwar ɓullar cutar Korona da ake samu, musamman a dalilin fitowar wata sabuwar nau’in cutar mai suna COVID 19 Omicron, ya sanya hukumomi a ƙasar Pakistan fitar da wasu sabbin matakai ga masallatai da sauran wuraren ibada a ilahirin ƙasar.

Sababbin matakan da aka sanar ranar Juma’a sun bayyana cewa mutanen da aka yi wa allurar rigakafin cutar ne kawai za a bari su gudanar da ibada a masallatai da sauran wuraren bauta. Sannan dole ne su sanya takunkumin rufe fuska watau (face masks).

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wata musulmar da ta yi batanci ga Annabi (SAW) a ƙasar Pakistan
Cutar Korona: An haramta wa wadanda ba su yi riga-kafin COVID-19 ba shiga masallatai a Pakistan

Haka kuma, ana buƙatar mutane a masallata su bayar da tazara a tsakanin su ta aƙalla kafa 6, kuma an buƙaci masallatai da su cire shimfiɗun su daga harabobin su.

An buƙaci tsofaffi da mutane masu fama da cutuka masu tasowa akai-akai da su gabatar da sallolin su a gida.

Sabon tsarin ya jaddada muhimmancin amfani da abin wanke hannu, tare kuma da yin salloli a buɗaɗɗun warare domin tabbatar da an daƙile cigaba da yaɗuwar cutar.

Haka kuma hukumar ta yi kira ga masu zuwa masallatai da su dinga yin alwalar su a gida, sannan ta buƙaci da a dinga yin gajeruwar huɗuba ranar Juma’a.

A cikin awanni 24 da su ka gabata, Mutane 7,678 ne a kasar Pakistan su ka kara kamuwa da cutar, waɗanda su ka ƙaru daga 6,808.

Wannan shine karo na biyu da aka taɓa samun ɓullar cutar da yawa a rana ɗaya tun lokacin da cutar ta fara a shekarar 2020.

Yanzu haka waɗanda su ka kamu da cutar sun haura mutane miliyan 1.35. Sannan kuma an yi gwaji kimanin 59,343 a cikin awanni 24 da su ka wuce. An samu karin waɗanda su ka kamu da ita da kaso 12.93%.

Alƙaluman da hukumomin da suka fitar sun nuna mutane 24 sun mutu a cikin sa’o’i 24 da su ka wuce. Gabaɗaya an samu asarar rayuka har guda 29,065.

Sai dai duk da ƙaruwar yawan masu cutar da ake samu, har yanzu manyan jami’ai sun ƙi sanya dokar ƙulle inda suke cewa tattalin arzikin ƙasar ba zai iya ɗaukar wani sabon kulle ba.

Kamar yadda wata ƙididdiga daga NOCC ta nuna, akwai masu ɗauke da cutar sama da mutane 57,000 wanda daga ciki akwai 961 waɗanda suke cikin tsaka mai wuya.

Kididigar ta nuna cewa birnin Karachi ne ke kan gaba da kaso 45.43%, sannan sai birnin Muzaffarabad ya zo na biyu da kaso 23.94%, da kuma birnin Islamabad mai kaso 18.91%.

An karrama Injiniya musulma, Dana Al-Sulaiman da ta ƙirƙiro na’urar gano cutar Daji

An karrama injiniya Musulma don ilimin ta na ƙirƙirar chip wanda ke iya gano nau’ikan cuta daji daban-daban a cikin jikin majinyacin, injiniyan Saudiyya Dana Al-Sulaiman ta sami lambar yabo ta “Innovators Under 35”.

A wata hira da tashar Alekhbariya, Injiniya Dana ta bayyana cewa, na’urar waccce aka yi da ƙananan allura da aka lulluɓe da wani abu sannan aka sanya shi a cikin fata, ya na da iya ɗaukar ruwa, da kuma gano kwayoyin cutar kansa ta hanya mai sauƙi kuma ba tare da lalata ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe