34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Da nasan haka zai kasance da ko auren shi ban yi ba, Matar wanda ya yi garkuwa da Hanifa

LabaraiDa nasan haka zai kasance da ko auren shi ban yi ba, Matar wanda ya yi garkuwa da Hanifa

Matar mutumin da aka ɗamke da laifin yin garkuwa da kuma kisan wata ƙaramar yarinya a Kano, Hanifa Abubakar ta bayyana yadda maigidan na ta ya yaudare ta ya kawo yarinyar gida kafin daga bisani ya halaka ta.

Matar ta bayyana cewa ƙarya mijin na ta ya sharara mata cewa iyayen yarinyar sun yi tafiya, shiyasa su ka damƙa masa amanarta kafin su dawo daga tafiyar da su kayi.

Hanifa
Da nasan haka zai kasance da ko auren shi ban yi ba, Matar wanda ya yi garkuwa da Hanifa

Ta dai bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Dala FM ta ruwaito.

“Cewa yayi mahaifiyar yarinyar tana koyarwa a makarantar sa, ta samu aiki a Saudiyya za ta je birnin tarayya Abuja ta sa hannu, shiyasa ta bashi ajiyar yarinyar kafin ta dawo”

“Ya faɗa min cewa iyayen mahaifiyar Hanifa mazauna Maiduguri ne kuma mijin ta dan kabilar Ibo ne shiyasa ba a kai mu su yarinyar ba sanda na tambaye shi dalilin da yasa matar ta bashi ajiyar yarinyar maimakon ta kai wa ‘yan’uwanta.”

A cewar ta, ta yi dana sanin auren mijin na ta a dalilin wannan ɗanyen aikin da ya aikata.

“Da na san haka zan zo na kasance da ni da yara na da ban aure shi ba” a cewar ta.

A na sa ɓangaren, Abdulmalik Muhammad Tanko wanda ake tuhuma da aikata wannan mummunan aikin na garkuwa da kuma halaka Hanifa, ya bayyana cewa sharrin shedan ne ya rinjaye shi.

Mansurah Isah ta fashe da kuka ta roki gwamnati ta yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama’a

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Mansurah Isah ta rushe da kuka kan kisan gillar da Abdulmalik Tanko ya yiwa Hanifa a jihar Kano…

Yayin da al’umma suka zuba ido suna jira su ga irin hukuncin da gwamnati za ta dauka akan Malamin makaranta Abdulmalik Tanko, wanda ya yiwa Hanifa kisan gilla, ta hanyar bata maganin bera ya kuma daddatsa gawarta ya binne, wasu mutane tuni sun fara nuna ra’ayinsu akan irin kisan da ya kamata gwamnati ta yiwa wannan mutumi.

A cikin makon nan ne dai asirin Abdulmalik Tanko ya tonu, bayan ya sace Hanifa ya boye ta a gidan shi tsawon kwanaki 47, daga baya kuma ya kasheta ta bayan ya karbi kudin fansa daga wajen iyayenta.

Mutane da dama sun nuna takaicin su, inda suke hawa shafukan sada zumunta suna Allah wadai da kuma tofin Allah tsine ga wannan rashin imani da Malamin makarantar ya yiwa dalibar ta shi.

A yayin da jaridar Labarun Hausa ke cigaba da bibiyar abubuwan dake wakana, ta gano wani bidiyo na fitacciyar jaruma Mansurah Isah, inda take rusa kuka da nuna takaici kan wannan lamari, inda ta roki gwamnati ta dauki tsattsauran mataki akan wannan azzalumin mutumi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe