34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yunwa na neman halaka mu sakamakon dokar hana fita da IPOB ta kakaba mana – ‘Yan Kudu sun koka

LabaraiYunwa na neman halaka mu sakamakon dokar hana fita da IPOB ta kakaba mana - 'Yan Kudu sun koka
  • Dokar hana shige da ficen da kungyar IPOB ta ke sa wa ba karami wahala da kangi yake jefa mutanen yankin ba
  • ‘Yan kasuwar da sai sun fita kullum kafin su samo na abinci ga iyalansa wanan rashin fitan yana jawo musu barazana sosia
  • ‘Yan kasuwa sun bayyana yanda suke asarar makudan kudade a duk ranan da dokar hana fitan ya faru

‘Yan kasuwa da masu sana’ar hannu a Awka, babban birnin jihar Anambra na kokawa kan yadda dokar zaman gida da haramtacciyar kungiyar Biyafara (IPOB) ta kakaba musu take hana su gudanar da harkokin su, inda ta bayyana cewa hakan ba karamin illa bane ga tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas.

A cewar su, tun da aka fara zaman-gida, da kyar suke iya biyan bukatun iyalinsu, ga matsananciyar yunwa da suke fama da ita.

Kungiyar IPOB ta bayyana cewa duk ranar Litinin da ma kowace rana da Nnamdi Kanu shugabansu ya gurfana a gaban kotu to fa wannan rana babu fita sai zaman gida sun yi hakan ne a matsayin daya daga cikin matakan tilastawa ga gwamnatin tarayya kan dole ta saki shugaban nasu.

Wata mata mai suna Misis Ngozi Ude, wacce ke sana’ar soya kosai a Awka ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa ta shafe shekaru mai tsayi tana sana’ar suyar kosai wanda dashi take ciyar da marayun ‘ya’yanta.

Yadda kungiyar IPOB ta hana mutane fita wuraren harkokin su a Kudu
Yadda kungiyar IPOB ta hana mutane fita wuraren harkokin su a Kudu

Ta ce da wanan sana’ar take biyan duk wani bukatun ‘ya’yanta tun bayan rasuwar mijinta shekaru biyar da suka gabata, ta ce dan abun da take samun da shi ta ke duk wani hidima.

“A cikin kwanaki ukun da suka gabata, an tilastawa kowa zama a gida gashi bamu da abinda zamu ci, ni da ‘yayana muna matukar shan wahala sosai, ba mu da abinci saboda sana’ar mu ta yau da kullum ce dole sai mun fita kafin mu samo abinda zamu sa a baki,” in ji ta.

Wani dan kasuwa, Mai suna Mista Chuks Obasi, wanda ke sana’ar sayar da jakunkuna na gwanjo, shi ma ya koka inda ya ce galibin su rayuwarsu ta dogara ne da sana’arsu ta yau da kullum, yana mai cewa duk ranar da ba su bude shaguna ba, to suna fuskantar kalubale.

Ya ce zaman gida a yankin Kudu maso Gabas ba karamin illa yake haifarwa ba don haka akwai bukatar a duba lamarin domin ceto talakawan yankin daga radadin da za a ayi magance shi.

“Wannan zaman-gidan ba karamin illa yayi mana ba ya yi ma rayuwar mu gibi mu da yan uwan mu. Ya kuma tarwatsa mana tattalin arzikinmu, kuma idan aka ci gaba da wanan zaman gidan to fa mutane ba karamar wahala zasu sha ba,” inji shi.

Wani mai sana’ar walda, Mista Chidi Okoye, wanda ya zanta da wakilinmu, inda yake bayyana cewa yana da ayyuka da yawa a shagon sa amma ba bu halin fita saboda dokar zaman gida da aka sa musu.

A cewarsa, wannan zaman-gidan ba shi da wani fa’ida musamman ga tattalin arzikin jihar, kuma idan aka ci gaba da yin hakan to fa rayuwar al’ummar yankin Kudu maso Gabas ba karamar nakasu zata fuskan ta ba.

“Tun daga ranar Litinin har yau ban je shago ba, gashi kuma kudaden hannun mu duk sun kare ga babu kayan abinci.

Dole fa kungiyar IPOB ta dawo ta sake dubi ga wanan tsari na dakatar da zirga-zirga don wanan zaman gida yana iya jawo babban illa ga mutane da tattalin arzikinsu ” inji shi.

Sai dai kuma wani matashi mai suna Mista Uche Mathew, ya ce shi fa wanan dokar zama gida bata dame shi ba, idan har ita ce kadai hanyar da za a iya cimma burin Biafra to fa shi ya ce a cigaba kawai.

A cewarsa, kowace gwagwarmaya dole ne mutane su ba da wani abu don samun cikar burinsu.

“Ko da dai muna shan wahala a yanzu, wannan ne abinda zamu girba a bisa tada hankalinmu da zamu yi. Saboda haka dole muyi hakuri har zuwa wani lokaci.

Wasu ’yan kasuwa a Anambra sun bayyana yanda suke asarar sama da Naira biliyan 25 a Onitsha a duk ranar da kungiyar IPOB tasa dokar kullen zaman gida.

Sun ce wannan dokar ba karamin rage yawan kwastomomi ta ke yi ba, lura da cewa wannan umarni ya tilastawa mutanen yammacin Afirka da ke ketarowa kasuwanci a shiyyar canja sheka zuwa Legas saboda fargabar hare-haren kungiyar IPOB.

An sa dokar hana zirga-zirga kwana hudu a Kudu maso Gabas kafin ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe