36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda makwabci na ya kashe ‘ya ta mai shekara 8 bayan na biya kudin fansa N3m – Magidanci daga Zaria

LabaraiYadda makwabci na ya kashe ‘ya ta mai shekara 8 bayan na biya kudin fansa N3m – Magidanci daga Zaria

Wani mutumin Zaria, Alhaji Shu’aibu Wa’alamu, ya bayyana yadda aka yi garkuwa da ‘yar sa ‘yar shekara 8 tare da kashe ta bayan ya biya masu garkuwa da mutanen kudin fansa Naira miliyan uku.

Da yake magana a wata hira da jaridar Vanguard, Shuaibu Wa’alamu ya ce an sace ‘yar sa, Asmau, a ranar 9 ga watan Disamba 2021, kuma da ta kasa komawa gida, ya kai kara ga ‘yan sanda.

Waalamu
Yadda makwabci na ya kashe ‘ya ta mai shekara 8 bayan na biya kudin fansa N3m – Magidanci daga Zaria

“Bayan wasu kwanaki, masu garkuwan sun fara kiran lamba ta suna neman N15m. Amma mun tattauna kuma na fara ba su N2m. Sun karbi kudin ne a unguwar Rigasa da ke Kaduna. Daga baya, sai suka sake kira na suka bukaci a ba wdaani N1.045m a matsayin kawai sharadin sakin ‘ya ta.

‘’Ban yi gardama ba na ba su kuɗin. Sai dai bayan sun biya kudin fansa kamar yadda aka nema a ranar 19 ga watan Janairu, sai suka kira ni suka ce min sun kashe ta ne kuma suka kashe wayar. Kun ga tun farko ina bin wadanda suka sace ta muna yin abin da suka ce saboda tsoron rasa ta, yanzu sun kashe ta .

“Na san wadanda suka sace ta suka kashe ta. Suna kewaye da mu. Ina da hujja mai ƙarfi. Na gaya wa ‘yan sanda. Kuma suna kan shi. Hasali ma an kama wadanda ake zargin,” inji shi.

A baya dai an ruwaito cewa sa’o’i kaɗan da ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban suka hada kai domin yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa yarinya Hanifa a Kano, al’ummar garin Zaria a jihar Kaduna sun shiga rudani lokacin da labarin ya bayyana cewa wata yarinya ‘yar shekara takwas mai suna Asma’u, an sace ta kuma aka kashe.

Yarinyar da ba ta da laifin komai ta shafe sama da wata guda a hannun su, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Sun ce “an yi zargin wani Kabir, makwabcin mahaifin Asmau, Alhaji Shuaibu Wa’alamu ne ya aikata laifin.”

Wani rubutu da Musa Ahmed ya wallafa a shafin sa na Instagram, ya nuna cewa an sace yarinyar ne a lokacin da ta ke kan hanyarta ta sayen katin cajiwaya.

Mai garkuwar ya nemi a biya shi Naira miliyan 3 a matsayin kudin fansa amma daga baya ya kashe yarinyar.

A cikin sakon da aka buga ta yanar gizo, an rubuta haka: “An sace ‘yar abokina, yarinya mai shekaru 8 a hanyarta ta siyan kati a unguwar mu.”

Kwanaki 42 da suka gabata ta kasance tare da waɗanda suka sace ta waɗanda suka bukaci a ba su N3m, amma suka kashe yarinyar a karshe.

An ce, watakila yarinyar ta gane mai garkuwa da mutane wanda ke zaune kusa da gidan su, a zahiri, kusan kullum tana wasa da yaran sa.

“Sun kira mahaifin ta jiya suna nema karin kudin da ya wajabta ya aika wani da kudin.

“A yayin da yake jiransu, mutumin ya fusata sosai saboda sanyin da daddare, ya kira mahaifin sa ya shaida masa cewa bai ga kowa ba tukuna. Sai mahaifin ya kira lambar ya ce su gaya masa gaskiya idan sun kashe yarinyar.

“Ga shi, sai suka ce, sun kashe ta, sun binne ta a cikin kabari marar zurfi, kwanaki 4 da suka wuce. Don takaita labarin, an kama wanda ake zargin da danginsa jiya.”

Ko da yake an ce an kama waɗanda ake zargin, ‘yan jarida na nan suna jiran martani daga hukuma.

Yunkurin yin luwaɗi yayi dani shiyasa na kashe shi, cewar wanda ake zargi kisan kai

Abdulsalam Ibrahim, wanda ake zargi da kashe Dr Obisike Donald Ibe, wanda likita ne mai shekaru 37 da ya yi aiki a Zenith Lab and Kidney Centre, Abuja, ya bayyana cewa ya halaka likitan ne saboda ya yi yunƙurin yin luwaɗi da shi.

Abdusalam Ibrahim, Fidelis Ezekiel da Philemon Hussaini su ne mutane ukun da ake zargi da haɗa hannu wajen halaka Dr Obisike da abokin sa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe