34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Dan sanda ya harbe yaro har lahira akan ya daukar masa ‘Pure Water’ guda 1

LabaraiDan sanda ya harbe yaro har lahira akan ya daukar masa 'Pure Water' guda 1

Wani fusataccen dan sanda ya harbe wani yaro har lahira, sakamakon jayayya da suka yi akan ruwan leda, a garin Kabba tsohuwa, dake karamar hukumar kabba/Banu cikin jihar Kogi, a safiyar ranar Asabar.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta hada, lamarin ya janyo gagarumin ganganko daga mutanen da suka fusata, abin da ya sa duk alamuran kasuwanci suka tsaya cak a garin da lamarin ya faru.

Wani shedar gani da ido yace, yaron ne ya dauki ruwan leda kwaya daya daga cikin motar dan sandan ba tare da sanin sa ba.

Halayyar yaron, bata yiwa dan sandan dadi ba, inda katobarar data biyo baya shine, dan sandan ya sauke fishinsa akan yaron, wanda a nan take ya bindige yaron har lahira.

Hukumar ‘yan sanda tace kare kansa yayi

A wani martani na gaggawa, kwamashinan ‘yan sanda na jihar Kogi, CP Edward Egbuka, yace abin da ake yadawa ya sha banban da rahoton da suka karba da kwamandan yankin da al’amarin ya faru.

Kwamashinan ya kara da cewa, dan sandan yayi kokarin kare kansa ne daga wajen marigayin, inda yayi alkawarin yin kwakkwaran bincike domin fito da gaskiyar abin da ya faru.

Da yake tabbatar da kisan, kwamashinan yace, gaskiyar lamarin zai fito ne kadai bayan anyi zuzzurfan bincike.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa, ‘yan sanda suna yin iya kokarin su domin dakatar da duk wata hatsaniya a sakamakon lamarin.

Yunkurin yin luwaɗi yayi dani shiyasa na kashe shi, cewar wanda ake zargi kisan kai

Abdulsalam Ibrahim, wanda ake zargi da kisan Dr Obisike Donald Ibe, wanda likita ne mai shekaru 37 da ya yi aiki a Zenith Lab and Kidney Centre, Abuja, ya bayyana cewa ya halaka likitan ne saboda ya yi yunƙurin yin luwaɗi da shi.

Abdusalam Ibrahim, Fidelis Ezekiel da Philemon Hussaini su ne mutane ukun da ake zargi da haɗa hannu wajen halaka Dr Obisike da abokin sa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Dr Obidike da abokin sa Mr Ezekiel Edoja mazauna layin D22, 24, Games Village, suna tare a gidan a ƙarshen watan Disambar 2021 lokacin da lamarin ya auku.

Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja CP Sunday Babaji, ya tasa ƙeyar waɗanda ake zargin da sauran wasu masu laifuka 16 a ranar Talata.

Kamar yadda CP Babaji ya ce:

“Tun bayan samun wannan mummunan labarin, rundunar ‘yan sandan Abuja ta kai gawawwakin zuwa ma’adana sannan ta miƙe tsaye wajen zaƙulo waɗanda suka tafka wannan ta’asar ta kisan mutum biyu a Games Village.

“Waɗanda suka kitsa wannan ɗanyen aikin sun yi awon gaba da abin hawa tare lalita mai ɗauke da kuɗi kimanin $1,000, wayar salula da katin bankin mamacin, wanda su kaƴi amfani da shi wajen cire zunzurutun kuɗade har naira miliyan biyu a asusun bankin mamacin a ranar 13 ga watan Disamban 2021.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe