36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Na yi alkawarin ba zan ci amanar ‘yan Najeriya ba idan har suka zabe ni shugaban kasa – Yahaya Bello

LabaraiNa yi alkawarin ba zan ci amanar 'yan Najeriya ba idan har suka zabe ni shugaban kasa - Yahaya Bello

Gwamann jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yiwa ‘yan Najeriya alkawari cewa ba zai taba cin amanar su ba idan har suka zabe shi shugaban kasa a zabe mai karatowa na shekarar 2023.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnan na jam’iyyar APC shine ya bayyana haka a ranar Alhamis 20 ga watan Janairu, a lokacin wani taro da aka gabatar na yankin Arewa maso Gabas a jihar Bauchi.

Jaridar Labarun Hausa ta gano cewa Yahaya Bello ya bayyana cewa ba zai bawa ‘yan Najeriya kunya ba, saboda shi mutum ne mai cika alkawari.

Zaben 2023: Yahaya Bello ya nuna kwarin guiwar lashe zabe

Gwamnan kuma ya kara da cewa yana da tabbacin cewa shine zai samu nasara a zaben mai karatowa, kuma shine zai fito da Najeriya daga halin da take ciki a halin yanzu.

Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi, mai neman takarar shugaban kasa a 2023, Yahaya Bello

Ya ce:

“Magana ake a kan mu, akan jam’iyyar mu, Najeriya da kuma mu a nan gaba. Amma cikin ikon Allah, tare da goyon bayanku da kuma addu’o’in ku, ina da tabbacin cewa zamu samu nasara.

Yahaya Bello wanda yayi magana da ‘yan majalisun ta wayar tarho, ya bayyana musu cewa bai samu halartar wannan taro bane da kanshi, saboda baya son ya karya doka.

Ya ce:

“Ina da niyyar zuwa wajen da kai na, amma ba na so a ganni ina karya doka, tunda har yanzu ba a bawa kowa damar gabatar da kamfen ba. Ina so na bi doka.

2023: Yahaya Bello ne ya cancanta, Tinubu ya yi hakuri ya ja da baya – cewar ITAN

Haka suma ‘yan kungiyar “Inter-Tribal Association of Nigeria” (ITAN), ta roki jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, da ya yi hakuri ya ajiye kudurinsa na fitowa takara ya goyawa Yahaya Bello baya.

Kungiyar ta bayyana Tinubu cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a bawa matasa dama su mulki kasar, inda ta kara da cewa Yahaya Bello yana kwarewa a fannin shugabanci.

Wannan roko da kungiyar tayi ya fito daga bakin mai magana da yawun kungiyar Kwamared Jabir Aminu Maiturare da kuma Sakataren kungiyar Simon Terna Anakaa, a wata sanarwa da suka fitar a Kaduna ranar Alhamis 20 ga watan Janairu.

‘Yan Najeriya za su samu ilimi kyauta da zarar na zama shugaban kasa – Bola Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin biyan kudaden jarrabawar kammala sakandare wato WAEC ga kowane dalibi dan Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta yada a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyon da ya bayyana inda ya ke jawabi ga wasu kungiyoyin mata ya bukaci da su ci gaba da zama a jam’iyyar APC domin ciyar da jam’iyyar gaba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe