27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Dandanon su daya da na kifi: Matar da ta mayar da Kyankyasai kayan kwalamar ta

LabaraiDandanon su daya da na kifi: Matar da ta mayar da Kyankyasai kayan kwalamar ta

Bayan ta tafka asara wurin kiwon kaji da agwagi, wata mawaƙiya mai suna Saumu Hamisi wacce aka fi sani da Ummy Doll ta koma kiwon kyankyasai.

Ta bayyana cewa akwai riba sosai a kiwon kyankyasan, sannan tana jindaɗin cin su a matsayin kayan kwalamar ta.

Hamisi ta bayyana cewa da farko ‘yan’uwan ta da maƙwabtan ta sun tsorata matuka, sai dai tuni su ka canza tunani bayan sun fuskanci ta na samu kuɗi a harkar.

Kyankyaso
Dandanon su daya da na kifi: Matar da ta mayar da Kyankyasai kayan kwalamar ta

Wata mata a birnin Dar es Salaam, na ƙasar Tanzania, ta zama abar magana a shafukan yanar gizo bayan ta mayar da kyankyasai abincin ta.

Matar mai suna Saumu Hamisi, mawaƙiya ce wacce aka fi sani da suna Ummy Doll, ta bayyana cewa mutane sun yi tsegumi sosai yayin da su ka ji cewa tana kiwon kyankyasan.
A cewar ta kyankyasai suna da ɗan karen daɗi kuma akwai riba sosai a kasuwancin su.

Ta samu makudan ƙudade da kyankyasai

“Wasu sun kira ni da mahaukaciya amma na samu kuɗi sosai da kyankyasai, saboda haka ko a jikina ba na damuwa da maganganun da mutane ke yi,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

Hamisi, wacce ta rera wata waƙa mai suna Sina, ta bayyana cewa kyankyasai na da ɗan karen daɗi.

“Yana ɗaya daga cikin kalar abincin da na fi so. Ana iya cin su ɗanyu, ana iya dafa su, sannan ana iya dafa su da Kwakwa ko a haɗa su da Ugali ko Shinkafa,” a cewar ta.

Mawaƙiyar ta bayyana cewa kyankyasai kamar kowanne irin abinci ne, sannan suna da ɗanɗano irin na kaza ko soyayyen kifi.

A cewar mawaƙiyar ta yanke shawarar komawa kiwon kyankyasai ne bayan ta tafka asara lokacin da ta ke kiwon kaji da agwagi.

Ana samun riba kwarai da kiwon kyankyasai

Saidai, Hamisi ta yi nuni da cewa kyankyasan da ta ke ajiyewa suna da bambanci da waɗanda ake samu a cikin gidaje.

“Na siyo waɗannan kyankyasan ne a wata ma’aikata a Morogoro. Ba su da cututtuka a jikin su, kuma ina tabbatarwa cewa suna cikin muhalli mai tsafta,” a cewar ta.

Ta gargaɗi mutane da kada su ci kyankyasan da su ke a cikin gidajen su. Hamisi ta bayyana wuraren da su ka fi dacewa da adana kyankyasan, waɗanda su ka haɗa da waje mai duhu, ɗumi sannan da kuma isashshen abinci.

“Su na da saurin girma da saurin haihuwa,” a cewarta.

Ta bayyana cewa ‘yan’uwanta da maƙwabtanta sun yi mamaki matuƙa a lokacin da su ka fahimci tana kiwon kyankyasai.

“Da farko maƙwabta na da ‘yan’uwa na sun razana matuka, sai dai yanzu sun saba da lamarin,” a cewarta.

Idan mijina yana neman mata zan sake salo ne na nuna masa soyayyar da zai daina tunanin wata mace – Shawara ga matan aure

Fitacciyar mai bada shawara kan sha’anin aure da soyayya ta kasar Ghana, Charlotte Oduro, ta shawarci matan aure da su daina barin mazajensu na yaudarar su, ta kuma gaya musu abin da za su yi don jawo hankalin mijinsu ya dawo gare su.

A wata hira da tayi da Kofi TVm masaniya a kan zamantakewar ta aure, ta ce rashin tunani ne ace mace ta bari wata ta zo har gida ta kwace mata miji, saboda haka ta nunawa mijinta soyayya ko da ace ya ci amanar ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe