36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wata musulmar da ta yi batanci ga Annabi (SAW) a ƙasar Pakistan

LabaraiKotu ta yanke hukuncin kisa kan wata musulmar da ta yi batanci ga Annabi (SAW) a ƙasar Pakistan

Wata kotu a ƙasar Pakistan ta yanke hukuncin kisa ga wata mata musulma bayan ta zagi annabi Muhammad (SAW) ta hanyar sanya wasu hotuna masu nuna ɓatanci kan fiyayyen halitta tare da ɗaya daga cikin matan sa.

Kotun mai zama a birnin Rawalpindi na arewacin Pakistan, ta yanke hukuncin kisan ne kan Aneeqa Ateeq ranar Laraba bisa dokokin ƙasar waɗanda su ka tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi batanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Yan sanda
Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wata musulmar da ta yi batanci ga Annabi (SAW) a ƙasar Pakistan

“Abubuwan ɓatancin waɗanda ake zargin ta da aikatawa sun hada da yin wata wallafa a WhatsApp da kuma tura saƙonni tare da zane-zanen ga wanda ya shigar da ƙara, inda yace sun yi muni a wajen musulmi” kamar yadda alƙali Adnan Mushtaq ya bayyana cikin hukuncin sa.

Ateeq mai shekaru 26, ta musanta dukkanin tuhumar da aka yi mata, wacce aka shigar a watan Mayun 2020.

A bayanin da ta yiwa kotu, Ateeq ta faɗa cewa wanda ya ke zargin na ta, Hasnat Farooq, da gangan ya janyo suka fara musu kan addini domin ya ja mata sharri bayan ta ƙi amsa tayin zama ƙawar sa. Su biyun sun haɗu ne a wurin buga wani wasa a yanar gizo inda daga bisani su ka cigaba da tattaunawa a WhatsApp.

“Ina zargin cewa da gangan ya kawo wannan maudu’in domin ɗaukar fansa, hakan ya sanya ya shigar da ƙara a kai na bayan ya gama haɗa dukkanin abubuwan da ya san za su zama matsala a gareni”, a cewar ta.

Farooq ya haƙiƙance akan cewa wacce ake zargin, ta yi munanan wallafe-wallafe a WhatsApp ɗin ta, sannan ta ƙi ta goge su bayan ya yi mata magana.

Babbar kotun Lahore ke da ikon tabbatar da hukuncin kisan da aka yankewa Ateeq, wanda kuma tana da damar ɗaukaka ƙara.

Ɓatanci dai a Pakistan ba abin wasa bane, inda ƙasar ta tanadi tsauraran dokoki akan laifukan da suka danganci yin ɓatanci waɗanda suka haɗa da hukuncin ɗaurin rai da rai da kuma hukuncin kisa kan zagin fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW)

Tun daga shekarar 1990, an kashe aƙalla mutane 80 a dalilin yin ɓatanci, kamar yadda ƙididdigar da Aljazeera ta yi ta nuna.

Waɗanda aka halaka sun haɗa da mutanen da ake zargi da yin ɓatancin, iyalan su, lauyoyi da kuma aƙalla alƙalai guda ɗaya.

An yanke wa ministan Pakistan hukuncin kisa kan ɓatanci ga Musulunci

Lahore, Pakistan – Wata kotun yankin da ke Rawalpindi da ke kasar Pakistan ta yanke wa wan fasto, Zafar Bhatti, mai shekaru 58 hukuncin kisa kan batanci kuma yana gidan kurkuku tun 2012.

An zargi shugaban da aika sakonnin kar ta kwana na zagin addini. An yanke wa Zafar Bhatti hukuncin daurin rai da rai a ranar 3 ga watan Mayun 2017 karkashin dokokin Penal Code na Pakistan kan wulakanta Annabi Muhammad da mahaifiyarsa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe