24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

‘Yan Najeriya za su samu ilimi kyauta da zarar na zama shugaban kasa – Bola Tinubu

Labarai'Yan Najeriya za su samu ilimi kyauta da zarar na zama shugaban kasa - Bola Tinubu
  • Jigon jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin biyan kudin WAEC ga daliban da zasu kammala sakandire
  • Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga wasu kungiyoyin mata na jam’iyyar APC a wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta
  • Tinibu ya bayyana cewa Najeriya na bukatar kwanciyar hankali domin samun cigaban mata din ganin sun ci gaba da gudanar da ayyukansu daban-daban

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin biyan kudaden jarrabawar kammala sakandare wato WAEC ga kowane dalibi dan Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta yada a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

Bola Tinubu

Ya ke cewa :

“Za mu biya kuɗaɗen jarrabawar ‘ya’yanku na WAEC ta yadda ba za a bar kowa a baya ba a harkar ilmi, komai talaucin sa.

“Alamar jam’iyyarmu ita ce tsintsiya. Alamar hulata kuma shine ba gudu ba ja da baya zamu kawo karshen jahilci, talauci, da sauran abubuwa.

“Muna bukatar kwanciyar hankali a kasa, muna buƙatar zaman lafiya, muna bukatar dakatar da ƴan ta’adda saboda yana da matuƙar mahimmanci, domin mata sune suka fi jikatta a tashin hankulan da ke afkuwa, zamu kawo karshen rashin zaman lafiya. Idan ba zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba za mu iya gina kasar yadda muke so ba.”

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyon da ya bayyana inda ya ke jawabi ga wasu kungiyoyin mata ya bukaci da su ci gaba da zama a jam’iyyar APC domin ciyar da jam’iyyar gaba.

A baya idan ba a manta ba munji cewa Bola Ahmad Tinubu ya fito ya bayyana ra’ayinsa nason tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya, ya fara bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kaima shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yake nuna cewa indai talakawa zasu ba shi damar wannan kujera to fa zasu ga sauye sauye da dama ciki hadda kawo karshen ta’addanci

Anji cewar Tinubu ya kai ziyara jihar Zamfara domin jajantawa ga hare haren ta’addanci da suke fuskanta, wanda har ya kai musu gudumuwar miliyoyin kudade, inda jama’a da dama suke ganin wannan ziyara daya daga cikin shirye shiryen kamfen dinsa ne.

Ina da tabbacin cewa zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 – Bola Tinubu

Bola Ahmad Tunibu ya bigi kirji cewa zai kawar da duk wani kalubale da ka iya kawo masa cikas wajen samun nasara a zaben Shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Tunibun yayi Wannan bugun kirjinne a ranar Asabar 15 ga watan Janairu 2022 bayan ziyarar da ya kai Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ya kara da cewa, yana da tabbacin shine zaiyi nasara a zaben Shugaban kasa mai zuwa, saboda gagarumin goyon bayan da yake dashi daga magoya bayansa.

Bola Ahmad Tunibu, na jamiyyar APC ya bigi kirjin cewa duk da kalubalen da yake fuskanta a takarar sa ta Shugaban kasa mai zuwa na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023 ; yana da tabbacin shine zaiyi nasara a karshe.

To masu karatu da wani fuska kuke kallon kokari da alkawarukan sa?

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe