34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Mansurah Isah ta fashe da kuka ta roki gwamnati ta yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama’a

LabaraiMansurah Isah ta fashe da kuka ta roki gwamnati ta yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama'a

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Mansurah Isah ta rushe da kuka kan kisan gillar da Abdulmalik Tanko ya yiwa Hanifa a jihar Kano…

Yayin da al’umma suka zuba ido suna jira su ga irin hukuncin da gwamnati za ta dauka akan Malamin makaranta Abdulmalik Tanko, wanda ya yiwa Hanifa kisan gilla, ta hanyar bata maganin bera ya kuma daddatsa gawarta ya binne, wasu mutane tuni sun fara nuna ra’ayinsu akan irin kisan da ya kamata gwamnati ta yiwa wannan mutumi.

A cikin makon nan ne dai asirin Abdulmalik Tanko ya tonu, bayan ya sace Hanifa ya boye ta a gidan shi tsawon kwanaki 47, daga baya kuma ya kasheta ta bayan ya karbi kudin fansa daga wajen iyayenta.

Mutane da dama sun nuna takaicin su, inda suke hawa shafukan sada zumunta suna Allah wadai da kuma tofin Allah tsine ga wannan rashin imani da Malamin makarantar ya yiwa dalibar ta shi.

A yayin da jaridar Labarun Hausa ke cigaba da bibiyar abubuwan dake wakana, ta gano wani bidiyo na fitacciyar jaruma Mansurah Isah, inda take rusa kuka da nuna takaici kan wannan lamari, inda ta roki gwamnati ta dauki tsattsauran mataki akan wannan azzalumin mutumi.

Mansurah Isah
Mansurah Isah

A bidiyon da Mansurah Isah ta saki a shafinta na tiktok, wanda kuma ta a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa:

Cikin kuka Mansurah Isah ta yi kira ga gwamnati

” Hanifa Ubangiji Allah ya jikan ki, Allah ya gafarta miki, Allah yasa kin huta, Allah yasa iyakacin wahalar da zaki sha a rayuwar ki kenan, Allah ya bawa iyayenki hakuri Hanifa.

“Mu muka gaza, haka kuma gwamnati ta gaza Hanifa. Ina rokon gwamnati ta sani wannan abu ya isa haka, mutanen da suke wannan abu ba ayi musu komai, ko an kai su gidan yari babu abinda ake yi musu, lokaci ya yi da ya kamata a dinga kashe su. A dinga rataye su a tsakiyar kasuwa kowa ya gani domin ya zama darasi ga na baya.

“Irin wannan yanzu mu iyaye ya zamu yi, ina zamu sa kan mu? Kalli yadda suka yanka ‘yar mutane kamar ba mutum ba.

“Gwamnati dan Allah dan Annabi muna rokon ku, ku taimaka mutanen nan a dinga daukar mummunan hukunci a kan su, iyaye muna cikin fargaba da tsoro, muna cikin tashin hankali.

Ka da hana danka fita, ka hana shi yin abubuwa da dama, a makaranta ma kuma bai tsira ba, wannan wace irin rayuwa ce haka, ya Allah ka fitar da mu daga cikin tashin hankalin nan.

“Gwamnati ku taimaka a kashe mutanen nan, a rataye su domin hakan ya zama izina ga masu son yin irin wannan abu, a yiwa wannan yarinyar da iyayenta adalci. Kada ku bari a kai su kotu, daga karshe a kai su gidan yari, daga baya kuma a sake su, mun roke ku dan Allah ku taimaka kuyi abinda ya dace akan wannan abu.

Daga baya kuma Mansurah Isah ta cigaba da wallafa rubutu a shafinta dake dangantaka da kisan na Hanifa, inda ta cigaba da kira da gwamnati ta dauki mataki akan lamarin.

Asiri ya tonu: Malama ta kashe dalibi da duka, makaranta ta yiwa iyayenshi karyar bashi da lafiya

A yanzu haka dai Abdulmalik Tanko na hannun jami’an ‘yan sanda, shi da sauran mutanen da aka kama dake da hannu da kisan Hanifa yarinya ‘yar shekara biyar kacal a duniya.

Haka kuma an samu damar zantawa da iyayen Hanifa, inda mahaifinta ya bayyana cewa ya dauki kaddara, domin kuwa dama ya san cewa dukkan mai rai mamaci ne, amma kuma ya ce ba zai taba mantawa da wannan abu ba a rayuwar shi, haka kuma ya roki gwamnati ta dauki mataki akan lamarin, ya kuma yiwa jami’an tsaro godiya kan kokarin su wajen bin diddigi akan lamarin.

Musu kan kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Barcelona ya sanya aboki ya kashe abokin shi a Katsina

An gurfanar da wani dan shekara 18 mai suna Idris Yusif, a gaban babbar kotun majistare ta jihar Katsina, a bisa tuhumar sa da kashe wani Saifullahi Abdullah, a kan musun kwallon kafa.

A cewar jaridar Punch, Saifullahi mai shekaru 28 ya mutu ne bayan musu da suka yi akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata, tsakanin Chelsea da Barcelona, inda daga baya, wannan musu ya rikide ya koma fada a tsakanin su, a ranar 12 ga watan Disambar shekara ta 2021, cikin karamar hukumar Danja dake jihar Katsina.

Mahaifin Saifullahi ya kai kara

Mahaifin mamacin, ya kai rahoton faruwar lamarin zuwa ga ofishin ‘yan sanda na Danja a ranar 20 ga watan Disambar 2021.

Yusif, wanda aka gurfanar dashi ranar Litinin a gaban babbar kotun majistare, ana tuhumar sa da laifin kisan kai. A karkashin sashi na 190, karamin sashi na(1) kamar yadda kundin tsarin doka na (penal code) ya tanada.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe