27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ahmed Musa ya bada tallafin N600,000 don cigaba da ginin babban Masallacin Garoua na kasar Kamaru

LabaraiAhmed Musa ya bada tallafin N600,000 don cigaba da ginin babban Masallacin Garoua na kasar Kamaru

Ahmed Musa wanda yake shine kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, ya bayar da tallafin kudi har Naira dubu dari shida (N600,000) don cigaba da ginin babban Masallacin Garoua na kasar Kamaru, yayin da kungiyar ta Super Eagles ke shirin karawa da kasar Tunisia a wasan zakarun Afrika.

Tsohon dan wasan Premier League din mutum ne mai bin addinin Musulunci, kuma a lokuta da dama yana nuna yadda yake da riko da addini ga masoyan sa domin kara musu karfin guiwa akan kowanne irin addini suka zaba.

A rahoton da jaridar Pulse da Platinum suka fitar, Ahmed Musa da Sadiq Umar duka suna zuwa babban Masallacin na Garoua tun lokacin da suka isa kasar ta Kamaru domin buga wasan zakarun Afrika.

Ahmed Musa
Ahmed Musa

Rahotanni sun bayyana cewa tallafin da Ahmed Musa ya yi, ya bayar ne domin cigaba da aikin ginin babban Masallacin na Garoua.

Wasanni nawa Ahmed Musa ya buga a zakarun Afrika?

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta Super Eagles ta buga wasanni uku a wasannin na zakarun Afrika a kasar ta Kamaru, inda kuma kungiyar ta samu nasarar lashe duka wasannin guda uku.

Ahmed Musa dai ya buga sau daya ne kawai, a lokacin da kungiyar take bugawa da kasar Sudan, kuma ana ganin cewa dan wasan zai samu damar buga wasu wasanni a nan gaba.

Shin Yaushe Najeriya za ta kara da kasar Tunisia?

Najeriya dai na kara daura damara yayin da ‘yan wasanta ke shirin fuskantar kasar Tunisia a kokarin da take na cin kofin zakarun Afrika na shekarar 2021.

Wasan karshe da Najeriya da Tunisia suka buga tare ya faru a shekarar 2019, a lokacin da kungiyar ta Super Eagles ta samu nasara akan kasar ta Tunisia, hakan ya ba ta damar zama kasa ta uku a wasan.

Kuna da ikon zama duk abinda ku ke so a rayuwa, don haka a rage tunani – Ahmed Musa ya aika sako ga masoyan shi

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Ahmed Musa ya hau shafin na kafar sadarwa don ya jawo hankalin masoyan shi, inda ya yi wani takaitaccen rubutu dangane da daraja da karfin da al’umma ke da shi a cikin zuciya.

Ya aikawa da masoyan shi sako

Gabannin fara wasan na su da kasar ta Sudan, Ahmed Musa ya aikawa masoyan shi wani sako a shafinsa na Instagram, inda yake cewa:

Har ya zuwa yanzu dai Ahmed Musa yana kan gaba, inda ya zama mutumin da yafi kowa zura kwallaye a tarihin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, inda ya zura kwallaye 103.

Haka kuma, Ahmed Musa ya fito ya bayyana cewa wannan wasa da suke bugawa na zakarun Afrika shine wasan da zai bugawa Najeriya na karshe.

Tsohon dan wasan gaba na Leicester City din, ya fara bayyana a cikin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya din a shekarar 2010, inda har ya zuwa yanzu yake cigaba da taka leda a kungiyar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe