Duka-duka mako biyu kenan, bayan ayyana yan fashin daji da suke addabar arewacin Nageriya a matsayin yan ta’adda, sai kuma ga jerin sunayen barayin da yaransu na jihar Zamfara ya bayyana.
Jaridar Vanguard ta hada rahoto cewa, wani farfesa a jami’ar Sokoto, Murtala A. Rufa’i, a wani littafin sa mai suna ‘I am a Bandit’ ma’ana (Ni Barawon Daji ne) ya lissafo sunayen shugabannin yan fashin da kuma adadin yaransu.
A fadar Rufa’i, an samo sunayen ne daga kauyuka daban-daban kusa da inda sansanonin yan ta’addan suke.

Karamar hukumar Muradun
- Sama’ila na Bayan Dutsi yana dayara 150 2. Jimmo Fadama na Bayan Ruwa yana da yara 80
- Simoli Jaya na Bayan Ruwa yana da yara 65
- Sahabi na Bayan Ruwa yana da yara 250
- Na’akka na Bayan Ruwa yana da yara 180
- Aminu Jajani na Bayan Ruwa yana da yara 120
- Sani Ba ruwanka na Dagwarwa yana da yara 135
- Uban Kafirai na Dagwarwa yana da yara 250
- Mai bokolo na Dajin ‘Yar Tunniya yana da mabiya 300
- Haruna Zango na Dammaka yana da mabiya 280
- Muntari na Duddubi yana da yara 31
- Ɓoyi na Dudduɗi yana da yara 210
- Turji na Fakai yana da kimanin mabiya 500
- Nakyalla na Filinga yana da mabiya 213
- Najana na Gidan Bisa yana da yara 96
- Sitanda na Gwari yana da yara 156
- Dullu na Sububu yana da yara 138
- Halilu Sububu na Sububu yana da sama da mabiya 1,200
- Maiduna na Tankyalla yana da mabiya 216
- Gwaska na Tungar Kolo yana da yara 76
- Kabiru ‘Yankusa na Safrar Kaɗe yana da yara 185
- Ƙaramin Gaye na Tungar Miya yana da yara 242
- Ɗan Sa’adiya na Dagwarwa da Bamako yana da yara 48
- Ɗan Shehu na Kudo yana da yara140
- Mati of Kudo yana da yara 165
- Ɗan Bello na Kudo yana da yara 98 Masarautar Dansadau
- Ɗan Makaranta na Madaka ta Arewa yana da mabiya 460
- Dogo Gyaɗe dake Dajin Babar Doka yana da kimanin mabiya 2000
- Damana a Dajin yana da kimanin mabiya1500
- Ali Kacalla na Madada yana da kimanin mabiya 1600
- Malam na Cebi ta yamma yana da kimanin mabiya 900
- Bulaki na ‘Yargaladima ta gabas yana da kimanin mabiya1200
- Ciyaman a ‘Yargaladima ta gabas yana da mabiya 900
- Ɗahe a ‘Yar galadima ta gabas yana da sama da mabiya 250 35. Kawu na gabashin Ɗansadau yana da sama da mabiya 700
- Ado Lalo na Ɗansadau ta gabas yana da 350
- Bulak dake Ceɓi ta gabas yana da kimanin yara 520
- Janburos na of east Madada ta gabas yana da yara 800
- Sani Bica dake gabashin Madaka yana da kimanin yara 180
- Ɗan Bagobiri na yammacinof Ceɓi yana da sama da yara 230
- Nagala dake Mairairai ta yamma yana da 750
- Ali ƙanen Nagala yana da yara 220
- Zahiru yana da 175
- Mai Gariyo dake kudancin Burwaye yana da yara 56
- Yalo na kusa da Burwaye yana da yara 85 Karamar hukumar Zurmi
- Kachalla yana da yara 1200
- Maidaji yana da yara 1500
- Ɗanƙarami yana da yara 750
Hotunan gwamnonin Arewa tare da rikakken dan bindiga da ya addabi al’umma ya jawo kace nace
Karamar hukumar Birnin Magaji
- Alhaji Zaki yana da yara 85
- Yalo na Rugu yana da yara 60
- Hassan na Rugu yana da yara 28
- Maidaji na Rugu yana da yara 40
- Kachalla na Rugu yana da yara 58
Karamar hukumar Shinkafi
- Atarwatse na Dajin Mashema yana da yara 200
- Ɗan Maƙwado na Kamarawa da Bafarawa yana da yara 550
- Nagona a tsakanin Bafarawa da Surduƙu yana da yara 200 Karamar hukumar Tsafe
- Idi dake Guga yana da yara 100
- Baba Yayi a Guga yana da yara 100
- Juuli na Kwankwanba yana da yara 100
- Tukur na Munhaye yana da yara 90
- Alhaji Ado Aleru dake Munhaye yana da kimanin yara 2500
- Mabi dake Munhaye yana da 100
- Ɗan’ Ibiro na Munhaye yana da yara100
- Guntu dake Munhaye yana da yara 65
- Karki dake Munhaye yana da yara 70
- Lawali Bunka dake Munhaye yana da yara 80
Shugabannin barayin da basu da takamaiman adadin yara
- Shehu Bagewaye
- Dancaki Odita
- Standard da Sani black
- Kabiru Maniya
- Malan Ila
- Rageb
- Kacalla Haruna
- Katare
- Hasan
- Husaini Jaja na Gusau
- Dogo Hamza na Bukkuyum
- Auta na Anka
Barayin da suka kware wajen aikata manyan laifuka, kama daga fashin daji, garkuwa da mutane, satar shanu, fashi da makami da kashe-kashen mutane, sun dade suna addabar arewacin Nageriya.
A wani rahotonni da suka bayyana a baya, barayin sun rubuta wasiku zuwa ga wasu al’ummu mazauna karamar hukumar Bukkuyum, a jihar Zamfara, cewa ko su biya kudi su tsira da ransu, ko su fuakanci hareharen yan ta’addan.
Yan fashin dajin Gando ne suka rubuta wasikun. An rubuta wasikun ne da Hausa kuma aka aika zuwa garuruwan.
Kowacce wasika tana dauke da sunan garin da aka tura zuwa garesu, a saman wasikar, da kuma kudin da zasu biya. Kuma an rubuta bambar waya da zasu kira.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com