27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Budurwa da aka dauka aikin shara da wanke-wanke tayi awon gaba gwala-gwalai na N14m, sati daya da fara aiki

LabaraiBudurwa da aka dauka aikin shara da wanke-wanke tayi awon gaba gwala-gwalai na N14m, sati daya da fara aiki

Wata ‘yar aikin gida wacce da Blessing kadai aka santa, tayi layar zana, bayan zargin da ake yi mata na satar kudi da gwala-gwalai, wadanda kimarsu zata kai kimanin Naira miliyan goma sha uku da dubu dari tara (N13.9m), daga gidan uwar gidanta da take yiwa aiki, wanda yake a Victoria Island a jihar Legas.

Uwar gidan Blessing din Pearl Ogbulu, a ranar Talata 18 ga watan Janairu, tace wadda ake zargin ta aikata laifin ne, mako guda kacal da fara yi mata aiki.

Tace ta shiga wasan buya da yarinyar ‘yar asalin jihar Cross-rivers dinne tun bayan faruwar lamarin.

Jaridar PUNCH Metro, sun hada rahoton cewa, Joshua Amaha, shine ya kawo Blessing din gidan Ogbulu, wadda bata gida, a ranar da yar aikin ta ziyarci gidanta domin tattaunawa da ita.

Ogbulun ta kara da cewa, iyayen ta, wadanda tare suke zaune dasu a gidan nata, su suka shiga da Blessing din cikin gidan. A yayin tattaunawar ne sai Ogbulun tace wa yar aikin, tana da jarrabawa da zatayi da kuma wasu cike-cike a wani ofishin ‘yan sanda. Domin shirye-shirye ma sunyi nisa. A Wannan lokacin ne yarinyar yar shekara 25 tayi amfani da lokacin da bana nan ta samu damar yi min sata.

Yunkurin yin luwaɗi yayi dani shiyasa na kashe shi, cewar wanda ake zargi kisan kai

Ogbulu tace;

“Mai yiwu wa tana da wani sunan amma dai mu tace mana sunanta Blessing. Sannan kuma tace da ana ce mata Ihi. Daga jihar Rivers take, kuma shekarar ta 25 da danta dan shekara daya. Ta fara aiki dani Lahadin da ta wuce, da misalin karfe takwas da rabi na yamma 8:30 pm.

“Dillalin da ya kawo min ita, ya fada mini zata zo ranar Asabar, domin mu gana da ita, amma ban gantaba, kawai kuma sai dillalin yace dani gatanan zata zo ranar Lahadi. Na jira ba ta zo da wuri ba sai na fita. Da na dawo wajen karfe daya da rabi, 1:30 na dare, wanda ya rage kwana daya inje wurin aiki. Na tattauna da ita, anan ne na gaya mata jarrabawar da zanyi da kuma cike-ciken.

“A ranar 13 ga watan Janairu, anyi bikin cikar shekara na kanina. Blessing tana tsaye a bene hawa na uku, a lokacin da na shiga dakina na dauko ambulan guda biyu dauke da kudi, dubu dari biyar 500,000 a guda daya, dayar kuma dubu dari biyu 200,000. Na baiwa kanina dubu hamsin (N50,000), sannan kuma na kara masa, shi da mahaifiyata kowannen su dala dari dari. $100. Sannan sai na ajiye ragowar kudin a dakina.”

Ogbulu tace taje wajen holewa, ranar Lahadi.

“Da na dawo daga wajen casu sai na shiga farfajiyar gidan, domin na kira babana ya bude kofa. Amma daya sakko domin ya bude, sai yace ai kofar ba’a kulle take ba. Sai babana yayi sauri ya duba dakin Blessing, sai yace Blessing ta tattara kayanta, ta gudu.

“Mai gadin gidan yace shi bai ga lokacin da ta fita ba. Ni na san na kulle dakina, amma nayi mamaki yadda naga kofa a bude. Da na tafi kai tsaye inda nake ajiyar kudi na; sai na tarar duk an kwashe ambulan din da kudaden suke ciki. An dauke agogunan hannu guda biyu wanda daya kudinsa ya kai dala ($5,500), har da dankunnen ‘yata wanda kudin sa ya kama kimanin $3,300. Sannan ta dauki dala dubu biyar ($5,000), fam 300, da kuma Naira dubu dari biyu (N200, 000). Ta kwashe duka gwala-gwalai na na kimanin kudi dala dubu goma, ($10,000).

Attajirar matar, tace, dillalin ya bata lambar wayar dan uwan Blessing din da adireshin sa amma lambar tana nuna (not reachable ) ma’ana bata kaiwa inda ake kira. Kuma an kasa samun adireshin inda gidan sa yake.

Ta kara da cewa, na tambayi lambar Blessing da adireshin ta a Ikorodu, sai dillalin yace gurin yana Ijede. Ya bani lambar babarta, wadda itama batayi aiki ba. Amma manhajar “true caller” tana nuna sunan Elebe. “

“Munje da motata har Ijede, inda muka ajiye ta a wani gidan man NNPC a nan Ijede din, kuma muka hau babur me kafa uku, domin duba inda adireshin gurin yake, amma bamu sami wani guri makamancin wurinba. Me babur din ma dubu bakwai da dari biyar (N7,500) ya cajeni.

“Na kira dillalin, amma yace shi babu abin da zai iya taimakon mu akan wannan lamari. Yace wai haka ta taba faruwa dashi a baya, haka ita ma waccan matar tasa aka kama shi, sai da ya shafe kwanaki a tsare a wajen ‘yan sanda. Na mika rahoton lamarin ga hukumar DSS da ta IRT.

“Duk wani kokari da nayi domin kiran Joshua ya faskara, saboda lambarsa bata shiga.

Kwamandan rundunar sashen fikira na ‘yan sanda Tunji Disu, yace;

“Har yanzu ban karbi korafi a hukumance akan lamarin ba”.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe