35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Yunkurin yin luwaɗi yayi dani shiyasa na kashe shi, cewar wanda ake zargi kisan kai

LabaraiYunkurin yin luwaɗi yayi dani shiyasa na kashe shi, cewar wanda ake zargi kisan kai

Abdulsalam Ibrahim, wanda ake zargi da kisan Dr Obisike Donald Ibe, wanda likita ne mai shekaru 37 da ya yi aiki a Zenith Lab and Kidney Centre, Abuja, ya bayyana cewa ya halaka likitan ne saboda ya yi yunƙurin yin luwaɗi da shi.

Abdusalam Ibrahim, Fidelis Ezekiel da Philemon Hussaini su ne mutane ukun da ake zargi da haɗa hannu wajen halaka Dr Obisike da abokin sa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Dr Obidike da abokin sa Mr Ezekiel Edoja mazauna layin D22, 24, Games Village, suna tare a gidan a ƙarshen watan Disambar 2021 lokacin da lamarin ya auku.

Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja CP Sunday Babaji, ya tasa ƙeyar waɗanda ake zargin da sauran wasu masu laifuka 16 a ranar Talata.

Kamar yadda CP Babaji ya ce:

“Tun bayan samun wannan mummunan labarin, rundunar ‘yan sandan Abuja ta kai gawawwakin zuwa ma’adana sannan ta miƙe tsaye wajen zaƙulo waɗanda suka tafka wannan ta’asar ta kisan mutum biyu a Games Village.

“Waɗanda suka kitsa wannan ɗanyen aikin sun yi awon gaba da abin hawa tare lalita mai ɗauke da kuɗi kimanin $1,000, wayar salula da katin bankin mamacin, wanda su kaƴi amfani da shi wajen cire zunzurutun kuɗade har naira miliyan biyu a asusun bankin mamacin a ranar 13 ga watan Disamban 2021.

“Bayan wannan, an kama mutane 3 da ake zargi masu suna, Abdusalam Ibrahim mai shekaru 26, Fidelis Ezekiel mai shekaru 27 da Philemon Hussaini mai shekaru 22.

“Waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zargin su. Za a tura waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.

Sai dai yayin da ya ke magana da manema labarai, Ibrahim ɗan asalin jihar Kaduna, ya faɗa cewa:

“Da adda na yi amfani wajen halaka shi. Likitan ɗan luwaɗi ne. Yayi yunkurin yin lalata da ni ta ƙarfi. Ya riƙe min tufafi sannan yayi kokarin cire min kaya, da na hana shi, sai ya fara zagi na.

“Daga baya na kira abokai na zuwa gidan domin su taimaka min na kwashe kaya na. Likitan ya siyo kayan sha da yawa waɗanda su ka sanya na bugu. Ni da abokai na mu ka ɗaure shi tare da abokin sa. A lokacin da abokaina su ka fita daga ɗakin, na dawo ɗauke da adda sannan nayi gunduwa-gunduwa da shi saboda abinda ya yi yunƙurin yi da ni.

Da aka tambaye shi ko zai iya ƙara haske kan yadda likitan ya yi yunƙurin yin luwaɗi da shi, sai ya kada baki yace:

“Ya shigo ɗaki na inda ya buƙaci da nayi masa tausa. Na gaya masa ba zan iya ba. Sai ya ce zai biyani in faɗi ko nawa na ke buƙata wanda ni kuma naƙi yin hakan.

Sauran ma su laifin ana zargin su da aikata laifukn da su ka haɗa da garkuwa da mutane, kwacen ababen hawa, kisan kai, fashi da makami, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuka.

Za a gurfanar da tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh a gaban kotu kan kisan ‘yan Najeriya

Kwamitin bincike da gano gaskiya ta kasar Gambiya, wacce shugaban kasar Adama Barrow ya kafa a shekarar 2017 ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, yana da hannu a kisan wasu ‘yan Afrika ciki kuwa hadda ‘yan Najeriya.

A wani rahoto da kwamitin ta fitar a kwanan nan, ta yi zargin cewa wasubakin haure ‘yan Najeriya Yahya Jammeh ya sanya manyan sojojin shi sun tsare su, inda daga baya kuma aka yi musu kisan gilla, rahoton The Nation.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe