27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Najeriya ta zama kasa ta 2 da al’ummar ta suka fi kowa farin ciki a nahiyar Afrika

LabaraiNajeriya ta zama kasa ta 2 da al'ummar ta suka fi kowa farin ciki a nahiyar Afrika

Ƙasar Finland ta arewacin nahiyar Turai kuma memba a tarayyar Turai, ta zama ƙasa mafi farin ciki a duniya. Wannan na ƙunshe ne a cikin ƙididdigar wata ukun ƙarshe na shekarar 2021, wanda rahoton hukumar farin ciki ta duniya ya tabbatar.

A cikin rahoton wanda Sustainable Development Solutions Network ta Majalisar dinkin duniya ta fitar, ba ƙasa ko guda daya daga nahiyar Afrika da ta shiga cikin jerin arba’in ɗin farko.

Farin ciki
Najeriya ta zarce ƙasar Ghana, ta zama ƙasa ta 2 a Afirka wacce mazaunan ta suka fi kowa farin ciki

Abin lura anan shi ne rahoton farin ciki na duniya yana dogara ne akan wasu ma’aunai na rayuwa da su ke auna walwala da jindaɗin al’umma.

Yayin duba da rahoton, Legit.ng ta haskaka ƙasashen Afrika goma da su ka shigo cikin jerin.

Kasar Mauritius

Mutanen Mauritius sun zo a matakin farko a matsayin mutanen da su ka fi farin ciki a nahiyar Afrika kamar yadda rahoton farin ciki na duniya ya zo.
Ƙasar wacce ta yi suna saboda kyawawan duwatsun tekun da ke cikinta ta samu maki 6.02, inda ta zama ƙasa ta 44 a duniya a cikin jerin.

Kasar Nigeria

Najeriya ta samu cigaba inda ta matsa gaba a cikin jerin. Najeriya ta ɗare mataki na biyu a cikin jerin ƙasashen nahiyar Afrika.

A rahoton da aka fitar na watanni ukun farkon shekarar 2021, Najeriya ta na a mataki na 17 a nahiyar Afrika.

Najeriya ta samu maki 5.5 a ma’aunin 0 zuwa 10 sannan ta zo ƙasa ta 59 a duniya.

Kasar Ghana

Ƙasar Ghana ta yankin yammacin nahiyar Afrika, ta zama ƙasa ta uku a nahiyar Afrika bayan an saka ta a matsayi na 65 cikin ƙasashe 95 a duniya. Ƙasar ta samu maki 5.32 cikin 10.

Kasar Côte d’Ivoire

Côte d’Ivoire, wacce ake kira da Ivory Coast ta zama ta hudu a nahiyar Afrika bayan ta zo ta 70 a cikin ƙasashen duniya. Ƙasar ta yammacin nahiyar Afrika ta samu maki 5.26 a ma’aunin 0 zuwa 10. A rahoton wata ukun farkon shekarar 2021, ƙasar ba ta shiga jerin ƙasashe 17 ɗin farko ba a nahiyar Afrika.

Kasar Cameroon

A mataki na biyar cikin jerin, ƙasar Kamaru ce. Ƙasar ta samu maki 5.24 cikin 10 sannan ta zo a mataki na 71 a duniya. Sai dai wannan koma baya ne, inda a rahoton baya ƙasar ta zo mataki na huɗu a nahiyar Afrika.

Sauran ƙasashen da suka zo a cikin goman farko a nahiyar Afrika sun haɗa da:

  1. Afirka ta kudu
  2. Zambia
  3. Morocco
  4. Tunisia
  5. Uganda

An kama tsohon Sanata da hannu a kisan shugaban kasa

An kama Jean Joel Joseph, tsohon dan majalisar dattawa na kasar Haiti wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin kisan shugaban kasar Jovenel Moïse a Jamaica. BBC ta ruwaito cewa hukumomin Jamaica a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, sun tabbatar da cewa sun kama Joseph ne a yammacin Juma’a, 14 ga watan Janairu.

Jami’in Constabulary Force dake Jamaica (JCF) a wata sanarwa sun bayyana cewa an kama Joseph ne tare da wasu mutane uku da ake zargin ‘yan uwansa ne kan laifin shige da fice. An bayyana cewa an kama joseph ne a wani gida a St. Elizabeth, wanda ke cikin wani karamin coci da ke kudu maso yammacin tsibirin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe