24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Hotunan gwamnonin Arewa tare da rikakken dan bindiga da ya addabi al’umma ya jawo kace nace

LabaraiHotunan gwamnonin Arewa tare da rikakken dan bindiga da ya addabi al'umma ya jawo kace nace
  • Yayin da ake ci gaba da samun karuwar ta’adanci a yankunan arewacin Najeriya, hotunan wasu gwamnoni tare da ‘yan fashi ya janyo cecekuce
  • Musa Kamarawa, Babban na hannun daman shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji ne aka gani a cikin hotuna tare da Gwamna Matawalle da Tambuwal
  • Sai dai gwamnonin biyun sun musanta wata alaka tsakanin su da ‘yan fashin duk da cewa masu ruwa da tsaki sun bukaci a gudanar da bincike a kansu

Masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun bukaci a gudanar da tsatsauran bincike kan alakar wasu gwamnonin arewa da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji, bayan da hotunansu da wani na hannun daman sa mai suna Musa Kamarawa ya bayyana a shafukan sada zumunta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an ga Kamarawa a cikin hotuna ba adadi tare da gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal tare da kuma mataimakin gwamnan Sokoto, Mannir Dan Iyya.

Jaridar Labaru Hausa ta lura cewa jihohin Zamfara da Sokoto suna daga cikin jihohin Arewa maso yamma da ke fuskantar matsalar tsaro, hare-haren ‘yan bindiga inda aka hallaka daruruwan rayuka tare da raba dubbai da muhallansu.

An kama Kamarawa a Abuja

Dan bindigar da ke cikin hotuna da aka dauka tare da gwamnonin, an kama shi ne a Abuja a watan Satumbar 2021 tare da wani Bashar Audu, wanda aka kama shi da tabar wiwi da ake zargin yana kai wa Turji da mutanensa, Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Inda ya ke shaida wa ‘yan sanda cewa akwai sanayya mai karfi tsakanin sa da Turji. ya kara da cewa, Turji yana da masu gadi sama da 100 dauke da makamai kewaye da shi ya kuma bayyana sunayen wadanda ke yi ma barayin safarar takalma da kakin sojoji, da kuma kayan maye, da dai sauran abubuwa.

An gano cewa kamarawa yana da dangantaka da tsohon gwamnan Sokoto, inda Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kamarawa yana matsayin da ne ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa. Mahaifiyar shi ta kasance kanwace ga tsohon gwamnan.

Bayanai sun nuna cewa Kamarawa, dan asalin karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto ne, ya na cikin wadanda Gwamna Matawalle ya fara tuntuba bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a 2019, domin samun maslahar yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga. Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta bayyana cewa an sada Kamarawa ga gwamnatin jihar Zamfara ne a lokacin da ake kaddamar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Yadda za’a samu galabar yaki da cin hanci a Najeriya – IBB

Wani makusancin gwamna Matawalle ne yake bayyana cewa gwamnatin zamfara bata san cewa kamarawa yana da sha’awar harkan ta’addanci ba bata ma san yana aiki da su ba.

Sai dai ya kasa tabbatar da gaskiyar fitar wata wasika da ke yawo a shafukan sada zumunta, wacce ke nuni da gwamnati ta bawa Kamarawa mukami a matsayin mataimaki na musamman ga gwamnan, shin gaske ne ko kuwa karya ne.

An tattaro cewa Kamarawa ne ya karbi mahaifin Turji daga hannun jami’an tsaro inda ya dankashi ga ‘yan fashin a watan Yuli shekarar da ta gabata wanda bayan hakan ne aka sace mutane 50 a matsayin ramuwar gayya ga kama mahaifin Turji da ‘yan sanda suka yi.

Wani mai ruwa da tsaki kuma babban malami a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato wanda dan asalin Shinkafi ta jihar Zamfara ne, Tijjani Salihu, ya ce hotunan sun nuna fa Kamarawa ba “karamin mai laifi ba ne.”

Salihu ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi bincike sosai akan shi sannan su gurfanar da duk wanda ke da alaka da shi a harkan ta’addanci, komai girmansa. Shima da yake mayar da martani, wani mashahurin Malamin addinin musulunci a jihar Sokoto yace yayi mamakin yadda aka karkata hankali kan Kamarawa bayan akwai manya manyan masu fada a ji wadanda suke makusanta da gwamnati amma suke ba ma ‘yan bindiga tallafi.

Gwamnonin Zamfara da Sokoto sun musanta alakarsu da Kamarawa

Mai magana da yawun gwamna Matawalle, Zailani Bappa, ya ce an dauki wanan hoton ne a lokacin zaman yarjejeniyar zaman lafiya da akayi da ‘yan bindiga.

Ya ce a lokacin hadda dan fashin nan mai suna Auwalun Daudawa yana wurin wanan zaman yarjejeniyar da akayi, shine musabbabin daukan wanan hoto. Bappa ya kara da cewa Hotunan ba su yi wani nuni da cewa Gwamna Matawalle yana da alaka da Kamarawa ko wani dan fashi da makami ba.

Haka zalika Muhammadu Bello, mai taimakawa Gwamna Tambuwal kan harkokin yada labarai, shima ya fito ya kare ubangidansa inda yace babu wata alaka tsakanin ubangidansa da Kamarawa.

Martanin ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta game da lamarin

Nuhu Muhammad Sani

“Yan siyasar mu na Arewa wasa kawai suke da rayuwar mu, su ne ke da alhakin kare mu amma ba ruwansu da hakan, shi ya sa ‘yan ta’addan ke cin karen su ba babbaka ba tare da wani hukunci ba, ’yan siyasar AREWA su ne ke da alhaki akan rashin tsaron da ke faruwa.”

Okafor Johnkingsley ya ce:

“Ga wadanda ba su biya haraji ba gara suyi su biya kafin lokaci ya kure musu.”

Mabrig Korie ya ce:

“Ba za ku iya raba ‘yan ta’ada da ‘yan siyasa ba a Arewacin Najeriya ‘yan bindigar su ne kayan aikin ‘yan siyasa da ake amfani da su don tayar da kura.

Ekott All Hanson:

“Kulum addu’a na Buhari ya gam wa’adinsa ya koma gida ya,huta domin kuwa matsalar Najeriya ‘yan Najeriya suka kirkireta saboda haka samun ingantaccen Najeriya zai kasance abu ne mai wuya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe