24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Birnin Michigan zai zama gari na farko a Amurka da gwamnatin Musulmi kaɗai za ta jagoranta

LabaraiBirnin Michigan zai zama gari na farko a Amurka da gwamnatin Musulmi kaɗai za ta jagoranta

Hamtramack, wani birni na Michigan ya zama birni na farko a tarihin Amurka da gwamnatin Musulmi kaɗai za ta jagoranta.

Akwai mazauna kusan dubun ashirin da takeas da ke zaune a cikin birnin.

An naɗa Amer Ghalib a matsayin musulmi na farko magajin garin. Shi ɗan gudun hijira ne wanda a baya ya yi aikin kiwon lafiya kuma an haife shi a Yemen.

OUFBDYRXPVBYHNGTEJNESZJ2IM
Birnin Michigan zai zama gari na farko a Amurka da gwamnatin Musulmi kaɗai za ta jagoranta

Garin Hamtramack manoman Jamus ne suka kafa shi kuma ya kasance al’ummar baƙi ta Poland, wanda kuma aka sani da Little Warsaw.

A cewar jaridar The Detroit Free Press, wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 100 da musulmi ya kayar da wani magajin garin Poland.

Jagoranci ya tabbatar da cewa kasancewar mafi rinjayen gwamnatin musulmi ba yana nufin mutanen wasu addinai ba su da wani haƙƙi ba. Mutanen da suka fito daga wasu addinai, Kiristanci, Bayahude da sauran su ana daraja su daidai, in ji su.

Dr Omar Atiq: Musulmi na farko da zai fara rike mukamin shugaban Kwalejin Likitoci ta kasar Amurka

Dr Omar Atiq shine dan kasar Pakistan na farko da za a bawa mukamin shugaban kwalejin likitoci ta kasar Amurka (ACP), kuma zai zama likita na biyu wanda ba dan kasar ba da zai rike wannan mukami. Za a gabatar da wannan zabe, duk da cewa bashi da abokin hamayya a watan Janairun shekarar 2022.

Ganin irin sunan da kwalejin ke da shi a fadin kasar Amurka dama duniya baki daya, mambobin kasashe sama da 145 na duniya, za su sanya wannan abu cikin kundin tarihin kasar Pakistan.

Kimanin mutane 154,000, duka wadanda suka yi karatu a fannin lafiya, da kuma kwararrun likitoci da suka yi rijista a kwalejin.

Dr Omar Atiq, wanda yake farfesa ne a fannin likitanci da ilimin otolaryngology, an bashi mukamin shugaban ‘yan kwamitin gwamnonin kwalejin a shekarar 2019. Yana daya daga cikin ‘yan wannan kungiyar tun a shekarar 1993.

Ya yi karatu a kwalejin likitoci ta Khyber, da kuma jami’ar Peshawar dake kasar Pakistan, inda a nan ne ya samu kwalin digirin shi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe