34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Idan mijina yana neman mata zan sake salo ne na nuna masa soyayyar da zai daina tunanin wata mace – Shawara ga matan aure

LabaraiAl'adaIdan mijina yana neman mata zan sake salo ne na nuna masa soyayyar da zai daina tunanin wata mace - Shawara ga matan aure

Fitacciyar mai bada shawara kan sha’anin aure da soyayya ta kasar Ghana, Charlotte Oduro, ta shawarci matan aure da su daina barin mazajensu na yaudarar su, ta kuma gaya musu abin da za su yi don jawo hankalin mijinsu ya dawo gare su.

A wata hira da tayi da Kofi TVm masaniya a kan zamantakewar ta aure, ta ce rashin tunani ne ace mace ta bari wata ta zo har gida ta kwace mata miji, saboda haka ta nunawa mijinta soyayya ko da ace ya ci amanar ta.

A cewar ta, laifin mata ne ya sanya maza ke cin amanar su a titi. Saboda haka a duk lokacin da mace ta gano cewa mijinta yana neman mata a titi, abu na farko da za ta fara yi shine ta gyara halin ta.

Charlotte Oduro
Charlotte Oduro

“Idan mijina ya ci amanata, ba zan bar gidan ba. Sai dai mu mutu tare ni da shi. Saboda zai iya yiwuwa halaye na ne ya sanya shi cin amana ta, saboda haka zan canja halayena na nuna masa soyayya sosai.” A cewar ta.

Princess Shyngle ta bawa mata shawara

Haka ita ma Princess Shyngle ta bawa matan aure shawara mai matukar muhimmanci, da za ta sanya su hana mazajen su cin amanar su.

Shyngle ta bayyana cewa idan mata suka rama abinda mazajen su suke yi musu, mazan za su fara shiga hankalin su a duk lokacin da suka yi tunanin cin amanar matayen na su.

Ta kuma kara da cewa hakan zai taimaka matuka wajen rage rabuwar aure tsakanin ma’aurata.

A cewar ta:

“Idan matan aure suka ci amanar mazajen su a lokacin da suka gane mazajen na cin amanar su, ina tabbatar muku da cewa mazan za su shiga hankalin su sosai kafin su sake cin amanar matayen su. Haka kuma za a samu raguwar mutuwar aure tsakanin ma’aurata.

“‘Yar karamar shawara ce tawa ga duka matan aure, Idan suka ci amana kuma ku ci amanar su. A lokacin za su fara canja halayen su. Ya kai mai shirin zama mijina, ina fatan kana karanta wannan. Ina muku fatan alkhairi.

Kada ku yi tsautsayin auren namiji da yake wanka sau 3 a rana – Budurwa ta shawarci ‘yan mata

Wata kyakyawar budurwa mai ban dariya ta bawa ‘yan mata shawarar da ta jawo akayi ta tafka muhawara a kafofin sadarwa na zamani.

A wani rubutu da ta wallafa a shafin ta na twitter, ta baiwa ‘yan mata shawarar da suyi watsi da maganar auren duk wani namiji mai wanka sau uku a rana.

Sai dai kuma wani abin mamaki, shine, jami’ar Harvard ta fannin likitanci dake kasar Amurka ta taba wallafa wani rubutu wanda yake kama da abinda budurwar ta, hakan ya sanya wasu ke ganin abinda budurwar ta fada gaskiya ne.

Budurwar ‘yar asalin kasar Ghana dake zaune a Najeriya ta jawo kace nace a kafar sadarwa ta Twitter, bayan ta samu da dama sun ba ta goyon baya kan wannan magana da tayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe