24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Zaman gidan yari ya yi riba fursunoni 605 sun haddace Al-Qur’ani Mai Girma a Dubai

LabaraiZaman gidan yari ya yi riba fursunoni 605 sun haddace Al-Qur'ani Mai Girma a Dubai
  • Fursunoni sunyi wa kansu karatun ta natsu a kasar Dubai inda suka dukufa neman ilimin Addini
  • Sun cigaba da neman ilimi a fannoni daban daban,wanda hakan ya farune da taimakon hukumar ilimi ta kasar
  • An yi kokarin sama musu ayyukan dogaro da kai a gidajen horo da gyaran hali

A cikin shekaru biyu da suka gabata fursunoni 605 ne suka haddace Al-Qur’ani mai tsarki a birnin Dubai, hedkwatan cibiyar kasuwancin Hadaddiyar Daular Larabawa.

A shekarar 2021 ne, fursunoni 1,228 suka samu ayyukan yi a bangaren ilimin addini, wasanni, da kuma wasu bangarori daban daban a babban sashen hukunci da cibiyoyin gyara na ‘yan sandan Dubai.

Ayyukan ilmantarwa da horarwa na fursunoni sun ƙunshi sassa hudu: Sashen Shirye-shiryen Ilimi, Sashen Kula da Addini, Sashen Ayyukan Wasanni, da Sashen Koyar da Sana’a. Inda ake kwadaitar da fursunonin da su koya kuma su iya karanta Al-Qur’ani mai girma. Kimanin fursunoni 605 ne suka haddace Al-Qur’ani mai tsarki a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Fursunonin sun kammala karatunsu a matakai daban-daban na ilimi hakan ya faru ne a bisa haɗin gwiwar yankin Ilimi na Dubai da kwalejoji na gida da na duniya, kuma an samar da ɗakin karatu mai dauke da sabbin nau’ikan littattafan karatu da suka dace.

Sashen Shirye-shiryen Ilimi shi ne yake ba da darussa iri-iri da shirye-shiryen horarwa ga fursunoni, kamar kwasa-kwasan fasahar kere-kere na bai daya, zane-zane, yadda ake shirya fina finai, yaren Ingilishi, yaren kasar Sin, sarrafa tunani, da kere-kere.

A bara, kimanin fursunoni 170 ne suka kammala kwasa-kwasan Ilimin kimiyya, sanan kuma 191 sun amfana da kwasa-kwasai a fannin koyarwa.

Babban gidan yari da ake tsare fursunoni a Dubai
Babban gidan yari da ake tsare fursunoni a Dubai

Manjo Janar Ali al-Shamali, babban darektan babban sashin kula da hukunci da gyara na ‘yan sanda Dubai, ya ce shirin yana da manufar bunkasa tare da kuma farfado da baiwa da fasahar fursunoni da kuma karfafa musu imanin su.

Shirye-shiryen sun kuma hada da magance matsalar tunani da abunda ya shafi kwakwalwa da kuma taimakawa wajen kawar da tsoro da tashin tashina ga fursunoni bayan an sake su.

Al-Shamali ya kara da cewa, suna kokarin ganin fursunonin sun samu sake da kuma rayuwa mai tsari a cikin al’umma.

Hadda kwasa-kwasan wasan motsa jiki, da suka hada da Jiu-Jitsu, Dambe, da Karate, sashen na shirya gasa duk shekara na wasannin motsa jiki a fage daban-daban, da suka hada da wasan kwallon kafa, wasan kwallon hannu, da wasan kwallon raga.

Bugu da kari, fursunonin sun kammala gasar tafiya na mil 50 a matsayin wani bangare na gasar motsa jiki na kwanaki 22 da ‘yan sandan Dubai suka kaddamar.

Baya ga waɗannan, nau’in matakan gyara, babban sashin ya kirkiro da darussa daban-daban ga fursunoni na 3D animation, aikin noma, wasan ban dariya na jarida, gyaran motoci, ƙirkiran zane, kula da lambu, ilimin tsarin gine gine, yankan karfe, dabarun zane, da yin abin rufe fuska.

Za a dawo da shan ruwa a Masallacin Annabi cikin watan Ramadana bayan shafe shekara 2 da dainawa saboda COVID

A yayin da watan Ramadana mai albarka ke cigaba da karatowa, hukumar kula da harkokin Masallacin Annabi dake Madinah, ta bayyana kudurinta na dawo da shan ruwa a cikin Masallacin bayan shafe shekara biyu ba a yi ba sakamakon annobar COVID-19.

Don ganin an kare lafiya da rayukan al’umma, hukumar ta dakatar da shan ruwa a Masallacin na Annabi tun a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2020, wanda ya yi daidai da shekarar 1441 ta Musulunci.

Hukumar lura da harkokin Masallacin za ta dawo da shan ruwa a cikin Masallacin cikin watan Ramadana dake karatowa.

Sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa iya wadanda aka bawa lasisin yin hakan ne kawai za su samu damar shiga domin su gabatar da ibada da kuma buda baki.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe