34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Dalar shinkafar ka ta karya ba za ta karawa jam’iyyar APC daraja ba a idon ‘yan Najeriya – PDP ta caccaki shugaba Buhari

LabaraiDalar shinkafar ka ta karya ba za ta karawa jam'iyyar APC daraja ba a idon 'yan Najeriya - PDP ta caccaki shugaba Buhari
  • Jam’iyyar PDP ta aibanta dalar shinkafan da gwamnatin shugaba Buhari ta kaddamar a garin Abuja
  • Jam’iyyar tana ganin wanan a matsayin sabon salon yaudara ne ga talakawa
  • Wanan batu ya fito ne bayan Shugaba Buhari ya kaddamar da Shirin inda PDP ta ke nuna cewa wanan ba zai taimakawa jam’iyyar APC da komai ba a zabe mai gabatowa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta soki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnatin ta, kan yadda suka sake kirkiro da wani shiri na bogi, domin sake yaudarar ‘yan Nijeriya, saboda ganin gabatowar zaben 2023, inda aka kaddamar da dalar shinkafa a Abuja, wanda jam’iyyar PDP tayi ma lakabi da dalar bogi.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da Rice Paddy Pyramid na Najeriya a filin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa dake Abuja; an kaddamar da shirin ne karkashin jagorancin babban bankin Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyar manoma shinkafa ta Nijeriya.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya rattaba sa hannun sa a yammacin ranar Talata mai taken, ‘PDP ta yi wa Buhari, APC tsiya kan kaddamar da dalar shinkafa ta bogi”.

Dalar shinkafa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a Abuja
Dalar shinkafa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a Abuja

A cewar Ologunagba, ‘yan Najeriya na sane da yadda jam’iyyar APC da gwamnatinta ke “kirkiro” dalan shinkafa ta bogi a inda ake dura yashi a cikin buhunan shinkafa a jera a kan ginin katako kamar yadda aka yi a jihohin da ke karkashin mulkin APC a yankin Kudu maso Yamma a shekarar 2018.

“Babu wani amfanin yin bikin dalar shinkafa ta karya da APC ta gudanar a Abuja. Abun kunya ne ganin yadda shugabannin jam’iyyar APC suka mara ma shugaban kasa Muhammadu Buhari baya ta hanyar sa shi kaddamar da dalar shinkafa ‘yar waje wanda akayi karyar cewa ta gida ce wanda manoman mu suka noma, don kawai a yi ma duniya karyar irin cigaban da aka samu a harkan noman shinkafa a cikin gida Najeriya.

“In dai har da gaske ne an samu habakar noman shinkafa a Najeriya kamar yadda APC ke kokarin ganin ‘yan Najeriya sun yadda da hakan, to mai yasa har yanzu farashin shinkafar bai sauko ba sai ma cigaba da tashin gwauron zabi da yayi daga Naira 8,000 kowace buhu a lokacin da PDP ta mika wa APC mulki a shekarar 2015 inda yanzu ya daga ya koma Naira 30,000 a yau?

“A bisa la’akari da cewa jam’iyyar PDP ta mayar da yankunan jihohi da aka fi samun ruwa zuwa manyan wuraren noman shinkafa da gonaki da injinan barzar shinkafa a fadin kasar nan, wanda hakan ya haifar da habakar noman shinkafan gida, da kuma samun rage shigo da kayayyaki daga kasashen waje tare da fansar da kaya akan farashi mai rahusa. A zamanin gwamnatin PDP,” mai magana da yawun jam’iyyar ya bayyana haka.

Ku Karanta: Yadda za’a samu galabar yaki da cin hanci a Najeriya – IBB

Ya kara da cewa, jam’iyyar APC ta gaza, da manufofinta na yaki da cin hanci da rashawa wanda har yanzu ake fama dashi, sun juyar da duk wani ci gaban da PDP ta samu a bangaren noma, wanda hakan ya jawo hauhawa da tsadar kayan abinci a yau.

Ya ce ’yan Najeriya za su iya tunawa yadda gwamnatin APC ta kasa kare rayukan manoma musaman lokacin da ‘yan ta’adda suka kashe sama da manoma 40 a jihar Borno kuma ba a dauki wani mataki ba.

“Saboda haka kaddamar da dala ta karya da APC ta yi ba komai bane illa gazawarsu da kuma, yaudara, ayyukan bogi da kuma nuna halin ko in kula ga halin tsadar kayan abinci da ake ciki, kashi 22.95 bisa 100 na hauhawar farashin kayan abinci wanda shi ya ja kasarmu ta samu ci baya.wanda hakan yasa Najeriya ta zama kasa ta 98 a cikin kasashe 107 wanda suke fama da yunwa a duniya.

Ya kara da cewa;

“Ganin yadda zaben 2023 ya ke karatowa, jam’iyyar APC na burin taga ta sa hannun jarinta, dalar shinkafa ta karya, farfaganda, ha’inci da karairayi wanda da shi sukayi amfani wurin kwace mulki a shekarar 2015,” in ji shi.

Ologunagba ya gargadi jam’iyyar APC da su sani cewa fa shekarar 2023 ba daya ba ce da shekarar 2015, ya kuma kara da cewa ‘yan Najeriya sun ga yaudarar da ta fi ta dalar shinkafa saboda haka wanan ba zai taimaka ma jam’iyyar APC da komai ba a zaben 2023.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe